Yan Najeriya Za Su Caɓa, Gwamantin Tinubu Ta Ware N1bn domin Tallafa Masu

Yan Najeriya Za Su Caɓa, Gwamantin Tinubu Ta Ware N1bn domin Tallafa Masu

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin rabon sama da Naira biliyan daya ga kananan yan kasuwa da matsakaitan sana’o’i
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa wannan shiri ne na gasar masu kananan sana'o'i satau MSME ta shekarar 2026
  • An ce za a bude shafin neman shiga gasar daga ranar 7 ga Afrilu zuwa 7 ga Mayun 2026, inda aka bukaci ‘yan kasuwa su gabatar da bukatunsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa za ta bude shafin da kananan yan kasuwa da za su samu tallafi a Najeriya.

Ta ce ta shirya rabon sama da Naira biliyan daya ga kananan yan kasuwa, matsakaita da masu kananan sana’o’i a karkashin gasar MSME ta shekarar 2026.

Tinubu ya ware makudan kudi don tallafawa yan Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan samar da ayyukan yi da MSMEs, Temitola Adekunle-Johnson, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai, cewar Punch.

Kara karanta wannan

JNI ta ce an kashe Musulmai 4, an nemi 10 an rasa a harin Filato

Yaushe za a bude shafin cika tallafin Tinubu?

Ya ce za a bude shafin neman shiga gasar daga ranar 7 ga Afrilu kuma za a rufe a ranar 7 ga Mayun 2026 yana kira ga ‘yan kasuwa su nemi shiga.

Adekunle-Johnson ya ce taken gasar ta bana shi ne “Renewed Hope for MSMEs,” inda aka fi mayar da hankali kan bayar da tallafin kudi domin bunkasa kasuwanci.

Ya kara da cewa:

“A bana muna mayar da hankali kan tallafi kai tsaye da zai taimaka wajen habaka kasuwancin watau MSMEs a fadin kasa baki daya.”

A cewarsa, shirin ya bambanta da na baya da suka fi bayar da kyaututtuka kamar motoci, gidaje da shaguna ga wadanda suka yi nasara.

Ya bayyana cewa sabon tsarin zai bai wa ‘yan kasuwa damar samun kudade kai tsaye bisa bukatunsu na gaggawa domin inganta harkokinsu.

Haka kuma ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar abokan hulda za su tabbatar da rarraba tallafin cikin gaskiya da kuma fadada yawan wadanda za su ci gajiyar shirin.

Kara karanta wannan

Watakila ADC ta gyara zama a Sokoto, Sanatan APC na tunanin sauya sheka

Ya kara da cewa ba wai mutum uku na farko kadai za su amfana ba, domin za a bai wa karin mahalarta damar samun tallafi.

Ka'idojin cike tallafin N1bn ga yan Najeriya
Shugaba Bola Tinubu yana rattaba hannu kan wata takarda. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Yadda tsarin ba da tallafin Tinubu ya ke

Adekunle-Johnson ya ce wadanda suka yi nasara za su kuma samu shirye-shiryen horaswa daga hukumomin gwamnati domin kara karfin kasuwancinsu.

Ya ce za a samar da shawarwari na kasuwanci da damar shiga kasuwanni bayan gasar domin tabbatar da dorewar cigaban wadanda suka amfana.

A cewarsa, wasu daga cikin fitattun ‘yan kasuwa za su samu damar halartar baje kolin kasa da kasa domin fadada harkokinsu, cewar The Guardian.

Ya ce za a duba kirkire-kirkire, samar da ayyukan yi, amfani da fasaha da kuma ingancin aiki wajen zabar wadanda za su yi nasara.

Adekunle-Johnson ya amince cewa a baya an samu matsaloli na rashin ingancin takardun neman shiga gasar daga wasu mahalarta.

Gwamnatin Tinubu za ta raba tallafin N180bn

A wani labarin, an ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirin HoPE-CT ya isa ga fiye da iyalai miliyan tara domin rage radadin talauci.

Kara karanta wannan

Ja'oji: Ana tsakiyar taron APC, 1 daga cikin manyan hadiman Tinubu ya yi murabus

Ministan Yada Labarai, Idris Mohammed ya sanar da cewa za a bai wa iyalai miliyan 3.6 tallafin kudi har N50,000.

A wani bangaren, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce za a bada lamuni marar ruwa har N400,000 ga mata da matasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.