Ana Kuka da Tsadar Mai, Dangote Ya Zaftare Farashin Litar Fetur

Ana Kuka da Tsadar Mai, Dangote Ya Zaftare Farashin Litar Fetur

  • Matatar Dangote ta sanar da rage farashin fetur a yayin da ƴan ƙasa ke kokawa da tsadar litar fetur
  • Farashin man daga bakin teku ya tsaya a kan N1,153, abin da ake ganin zai sauƙaƙa jigilar kaya ta ruwa
  • Ana sa ran sauyin zai shafi tsarin rabon mai a faɗin Najeriya bayan masu abubuwan sufuri suna kokawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa

Jihar Lagos– Matatar Dangote ta sanar da rage farashin fetur da ake sayarwa daga matatar zuwa N1,200 kan kowace lita.

Haka kuma, ta kayyade farashin da ake daukosn daga bakin teku zuwa N1,153 kan kowace lita, wanda ya sauka a kan farashin baya.

Matatar Dangote ta rage farashin mai
Motar man fetur ta matatar Dangote Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa a na kallon wannan sabon mataki a matsayin wani muhimmin sauyi da zai iya tasiri kai tsaye ga yadda ake sayar da mai ga ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Matakai 4 da Najeriya ta dauka bayan fara yakin Iran, Amurka da Isra'ila

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur

The Cable ta wallafa cewa mai magana da yawun rukunin Dangote, Anthony Chiejina, ya bayyana cewa wannan sauyin farashi wani ɓangare ne na sake fasalin tsarin farashin da matatar ke amfani da shi.

A cewarsa, matakin ya zo ne a daidai lokacin da kasuwar man fetur ta duniya ke fuskantar rashin tabbas, sakamakon rikice-rikicin Gabas ta Tsakiya, waɗanda ke tasiri ga farashin mai a duniya.

Ya ce, rage farashin zai taimaka wajen sauƙaƙa farashin samar da fetur a cikin sarkar rarraba mai, daga matata zuwa wuraren ajiya da kuma gidajen mai.

Tasirin sauyin farashin man Dangote

Da sabon farashin N1,200 a kan kowace lita, ana sa ran ‘yan kasuwa da masu shigo da mai za su sake lissafin kuɗin da suke kashewa.

Wannan zai yi tasiri musamman ga waɗanda ke sayen mai daga cikin gida maimakon shigo da shi daga ƙasashen waje.

Haka kuma, farashin bakin teku na N1,153 zai ba da damar sauƙaƙa jigilar fetur ta ruwa zuwa tashoshin ajiya da ke yankunan Kudu, wanda hakan zai buɗe wata hanya ta daban ga masu rarraba mai.

Kara karanta wannan

Allah mai iko: Wata mata ta haifi 'yan 5 rigis a Kano, gwamnati ta dauki mataki

Ana sa ran rage farashin zai nuna a gidajen man Najeriya
Motocin man Dangote tare da wani ma'aikacin matatar Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Ana ganin cewa wannan mataki na iya taimakawa wajen rage tsadar fetur a wasu yankuna, idan aka yi la’akari da raguwar kuɗin sufuri da kuma sauƙin samun mai daga cikin gida.

Sai dai kuma, har yanzu ana sa ido kan yadda wannan sauyi zai shafi farashin da masu amfani da fetur ke biya a gidajen mai, kasancewar akwai wasu abubuwa kamar sufuri, haraji da kuma riba da ke tasiri ga farashin.

Rage farashin daga matatar Dangote na iya zama wata muhimmiyar hanya ta daidaita kasuwar mai a Najeriya, musamman idan aka ci gaba da samun sauƙin samar da mai daga cikin gida.

Dangote ya fitar da mai zuwa waje

A baya, mun wallafa cewa rikicin Gabas ta Tsakiya ya jawo an samu kalubale wajen samun kayayyakin makamashi a duniya, musamman saboda barazanar rufe Hormuz.

Matatar Dangote da ke jihar Legas a Najeriya ta fitar da tataccen man fetur zuwa kasashen nahiyar Afrika da suka hada da Côte d’Ivoire, Kamaru, Tanzaniya, Ghana, da Togo.

Tura man fetur din ya kasance lokaci na farko da matatar ta fara fitar da shi zuwa wajen tun bayan da ta kai matakin tace gangar danyen mai 650,000 a kowace rana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng