Allah Mai Iko: Wata Mata Ta Haifi 'Yan 5 Rigis a Kano, Gwamnati Ta Dauki Mataki

Allah Mai Iko: Wata Mata Ta Haifi 'Yan 5 Rigis a Kano, Gwamnati Ta Dauki Mataki

  • Wata matar aure, Hafsatu Yusuf ta haifi yan biyar maza uku da mata biyu a asibitin Murtala dake Kano yayin da dukkaninsu suke cikin koshin lafiya
  • Mahaifin jariran wanda yake tuka Keke-Napep ya nuna farin cikinsa tare da godewa Allah bisa wannan kyauta ta bazata da ya yi masu
  • Gwamnatin jihar Kano ta sanar da daukar cikakken nauyin kudaden maganin mahaifiyar da jariran nata domin tabbatar da kula da lafiyarsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Wani abin mamaki da farin ciki ya faru a asibitin ƙwararru na Murtala dake birnin Kano, inda wata mata mai suna Hafsatu Yusuf ta haifi jarirai biyar rigis.

Mijin matar, Malam Salisu Nafiu, wanda matukin Keke-Napep ne, ya tabbatar da cewa matarsa ta haifi maza uku da mata biyu da misalin ƙarfe 2:00 na rana a jiya Laraba.

Kara karanta wannan

Zai shiga APC ne? Sule Lamido ya bude kofar ganawa da Shugaba Bola Tinubu

Wata mata ta haifi 'yan 5 a Kano
Lamia, wadda ta haifi 'yan 5 a asibitin Advocate Hemayet Uddin Ahmed Diabetic & General Hospital a Barishal, Bangladesh. hoto: Niamul Rifat/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Wata mata ta haifi 'yan 5 a Kano

Malam Nafiu ya bayyana tsananin godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki bisa sauƙa lafiya da aka samu, inda ya bayyana cewa wannan ita ce haihuwa ta tara da matarsa ta yi, a cewar rahoton Daily Trust.

Game da wani kabakin arziki da gwamnatin Kano ta yi masu, Malam Nafiu ya ce:

“Wannan tallafi ya zo a daidai lokacin da iyalina suke buƙatarsa, kuma muna matuƙar godiya ga gwamnati.”

A halin yanzu, jariran da mahaifiyarsu suna cikin ƙoshin lafiya ƙarƙashin kulawar likitoci na musamman.

Taimakon gwamnati ga uwar 'yan 5

Biyo bayan wannan haihuwa ta bazata, gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa za ta ɗauki cikakken nauyin kuɗaɗen magani da dukkan kulawar da mahaifiyar da jariran nata ke buƙata.

Kakakin ma'aikatar lafiya ta jihar, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnati na rage mace-macen mata da jarirai a jihar.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Tinubu ya tsallake rijiya, an gano wani mugun shiri da sojoji suka yi na kwace Aso Rock

A cikin wata sanarwa, wadda jaridar Punch ta samu, ma'aikatar lafiya ta Kano ta ce:

“Za mu ci gaba da tallafa wa al'umma, musamman marasa ƙarfi, domin tabbatar da cewa sun sami damar yin amfani da ingantaccen kiwon lafiya.”

Wannan karamci ya sa iyalai da dama a jihar yaba wa gwamnatin bisa sanya ido kan halin da masu ƙaramin ƙarfi ke ciki.

Gwamnatin Kano ta dauki nauyin kula da lafiyar jarirai 5 da mahaifiyarsu a asibitin Murtala.
Jarirai 5 da wata mata, Hafsatu Yusuf ta haifa a asibitin Murtala da ke Kano. Hoto: @NigeriaStories
Source: UGC

Abin sani game da haihuwar 'yan 5 rigis

Haihuwar 'yan biyar abu ne da ba a cika samu ba, musamman ta hanyar juna biyu na gida ba tare da an yi amfani da magungunan ƙara haihuwa ba.

Mafi yawan lokuta, ana haifar irin waɗannan jarirai ne kafin lokacin haihuwarsu na asali ya cika, kuma akan yi amfani da tiyata wajen fito da su, kamar yadda aka gani a takardar bincike da Dr. Styliani Salta da wasu mutum uku suka gudanar da aka wallafa a shafin Research Gate.

Saboda ƙanƙantarsu, jariran kan buƙaci kulawa ta musamman a sashin kula da jarirai (NICU) domin tabbatar da numfashinsu da girman jikinsu ya daidaita.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

'Yar Najeriya ta haifi 'ya'ya 5 lokaci guda

A wani labarin ma, mun ruwaito cewa, wata mata ƴar Najeriya ta samu kyautar ƴaƴa biyar, kuma ta bayyana hakan a shafukan sada zumunta.

A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta, matar mai amfani da sunan @ebyfullmoon, ta bayyana cewa ta samu ƙaruwar ƴan mata biyu da maza uku.

Fitowar cikinta ya ɗauki hankulan masu amfani da yanar gizo, inda suka yaba mata kan yadda ta iya ɗaukar cikin har na tsawon wata tara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com