Baiwa daga Allah: Matar da ta haifa 'ya'ya biyar a lokaci daya

Baiwa daga Allah: Matar da ta haifa 'ya'ya biyar a lokaci daya

- Baiwar haihuwa Allah kadai ke badawa kuma yana bata ne a lokacin da ya so

- Susan Egenti mata ce da ta yi shekaru 16 da aure ba tare da ta taba koda batan wata ba

- Ubangiji ya albarkaceta da 'yan biyar a lokaci daya bayan shekarun da tayi tana neman magani

Farin cikin kowacce mace ne a kirata da uwa bayan aure. Wasu wannan farin cikin ba ya samuwa, saboda rashin haihuwa na shekaru da yawa bayan aure.

Susan Egenti mai shekaru 44 bata samu wannan farin cikin ba sai bayan shekaru 16 da aure. Egenti ta haifa yara biyar ne a lokaci daya a asibitin tarayya da ke Jabi, Abuja.

Susan Egenti 'yar asalin karamar hukumar Anambra ta gabas ne da ke jihar Anambra. Ta haifa yaran biyar ne ta hanyar aikin da likitoci suka yi, suka cirosu daga cikinta.

DUBA WANNAN: Abba Gida-Gida ya yi martani a kan hukuncin kotun daukaka kara

'Yan biyar din sun hada da maza uku da mata biyu. Suna sashin bada kula na musamman da ke asibitin, kamar yadda wakilin jaridar Daily Trust ya kai ziyara ranar Alhamis.

Duk da dai, malaman jinyar da ke kula dasu sunce lafiyarsu kalau, amma akwai daya daga ciki wanda nauyinsa bai kai ba.

A yayin tattaunawa da Egenti da ke gadon asibitin, tace babu irin maganin da bata yi amfani dashi ba wajen ganin ta samu ciki, amma shiru. Tace haihuwar 'yan biyar dinta babbar baiwa ce daga Ubangiji, don ko batan wata bata taba yi ba kafin samun cikinsu.

Ta bayyana yadda ta kusa rasa ranta wajen haihuwarsu, don sau biyu aka yi mata aiki bayan haihuwarsun. Tace aikin karshe ya barta a mace na kwanaki biyar kafin ta farfado.

Ta yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su taimaka don ganin rayuwar yaran ta inganta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel