Kwalliyar Sallah Ta Jefa Matasa a Matsala, Hisbah Ta Kama sama da Mutum 600 a Kano

Kwalliyar Sallah Ta Jefa Matasa a Matsala, Hisbah Ta Kama sama da Mutum 600 a Kano

  • Hukumar Hisbah ta kama sama da mutum 600 kan bisa zargin aikata laifuffuka da suka saba da koyar wa addinin Musulunci
  • An cafke matasa da 'yan mata kan rashin da’a, tare da direbobin adaidaita sahu yayin da aka fara shagalin bikin Sallah karama a jihar
  • Haka kuma hukumar ta tsinci yara da dama da suka bace sannan ta sada su da iyayensu tare da gargadi a kan yanayin bikin Sallah karama

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ta kama mutane sama da 600 a sassa daban-daban na jihar.

Ta bayyana cewa an kama mutanen ne a yayin bukukuwan Sallah da suka gabata, bisa laifuffuka da suka haɗa da rashin da’a da ayyukan da suka saba al’ada.

Kara karanta wannan

Lamari ya kwabe: Saudiyya ta kori sojoji, jami'an diflomasiyyar Iran daga kasar

Hisbah ta kama masu shigar banza a Kano
Shugaban hukumar Hisbah na Kano Aminu Ibrahim Daurawa a wajen wani wa'azi Hoto: Imam Dr. Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Mataimakin babban kwamandan Hisbah, Dakta Mujahiddin Aminuddin, ne ya tabbatar wa manema labarai hakan.

Kano: Hisbah ta kama masu shigar badala

Jaridar Leadership ya shaida wa manema labarai cewa kamen ya kasance wani ɓangare na ƙoƙarin kare tarbiyya da al’adun al’umma a lokacin shagulgulan Sallah. Ya ce hukumar ta tura jami’ai sama da 9,500 a faɗin Kano domin sa ido a kan yadda ake gudanar da bukukuwan. A cewarsa, daga cikin waɗanda aka kama akwai matasa 275 da ake zargi da yin askin da bai dace ba da direbobin adaidaita sahu 85 da aka kama saboda ɗaukar mata a gefensu.

Haka kuma jami'an Hisbah sun kara kama mutum 21 da suka sanya gajerun wanduna, da kuma mata 286 da aka kama saboda rashin da’a wajen sanya kaya.

Dakta Mujahiddin Aminuddin:

“An kuma kama wani shugaban ƙaramar hukuma a wani otel tare da yara ba tare da izinin iyayensu ba. Daga baya mun kira iyayen, mu ka haɗa su da ‘ya’yansu, sannan aka sake su.”

Kara karanta wannan

Iran ta yi iƙirarin kai harin bama bamai wasu sansanoni a UAE da Kuwait, ta fadi dalili

Hisbah ta gargadi jama'a

Dakta Mujahiddin Aminuddin ya ce akwai wasu laifuffuka da suka haɗa aikata daba, sannan an kama wani matashi da ake zargi da samar da masauki domin zina da luwadi.

Babban jami'in ya kara da cewa an kuma kama wani ɗan kasuwa da ake zargi da adana makamai domin ba wa ‘yan daba, da kuma wani boka da ya aurar da wata budurwa ba tare da amincewar iyayenta ba.

An kama matasa maza da mata a kan laifuffuka daban-daban da Sallah
Taswirar jihar Kano inda aka kama wasu matasa da Sallah Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hukumar ta kuma yi nasarar haɗa yara 66 da suka ɓace da iyayensu, tare da tarwatsa wasu matasa da ke shirin shirya wani biki a yankin Sabon Gari.

Mataimakin Kwamandan ya jaddada cewa ya kamata Sallah ta kasance lokaci na neman gafara da ibada ga Musulmi, ba lokacin aikata abubuwan da suka saɓa wa koyarwar addini ba.

Ya ce:

“Duk waɗannan abubuwa sun saɓa wa al’adunmu da dabi’unmu. Muna gargaɗin masu wuraren taro da kada su karɓi bakuncin abubuwan da suka saba wa ƙa’idodinmu. Haka kuma muna kira ga jama’a da su taimaka ta hanyar kai rahoton duk wani abu mara kyau domin mu tsaftace Kano.”

Kara karanta wannan

"Yan ta'adda na amfani da bidiyon azabtarwa don firgita al’umma": Masani ya bayar da mafita

Jami'an Hisbah sun kama matasa

A baya, mun wallafa cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama matasa biyar bisa zargin daura wa abokansu aure ba tare da amincewar iyaye ba lamarin da ya saba doka.

Wasu rahotanni sun bayyaan cewa daga cikin wadanda aka kama akwai amarya, ango, da wasu uku da suka shiga wajen shaidar auren da waliyyansu.

Hisbah ta byyana cewa an yi auren ne da sadaki na ₦10,000 wanda bai kai ka’idar da Musulunci ya tanada ba, tare da daukar matakin ladabtar wa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng