Tsohon Akanta Janar Ya Sha Dauri, Zai Yi Zaman Shekaru 72 a Kurkuku saboda Almundahana
- Kotu a Abuja ta yankewa tsohon mukaddashin Akanta Janar a Najeriya, Chukwunyere Nwabuoku, hukuncin shekaru 72 a gidan yari
- Kotun ta tabbatar da cewa ta samu Mista Chukwunyere Nwabuoku da laifin karkatar da kudin tsaro da suka haura N868m
- An samu damar tabbatar da laifin da yanke hukuncin bayan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta gabatar da hujjojinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci kan tsohon mukaddashin Akanta Janar na Tarayya, Chukwunyere Nwabuoku.
Kotun ta tabbatar da yanke masa hukuncin dauri a gidan yari na tsawon shekaru 72 bisa samunsa da laifin zamba.

Source: Twitter
Daily Trust a wallafa cewa haka kuma an samu Chukwunyere Nwabuoku da laifin halasta kudin haram da almundahanar kudin tsaro da suka kai Naira miliyan 868.
Kotu ta daure tsohon Akanta Janar
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa alkalin kotun, James Omotosho, ya yanke hukuncin a ranar Litinin 23 ga watan Maris na shekarar 2026.
Da ya ke yanke hukunci, ya bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta gabatar da hujjoji masu karfi da suka tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi masa.
A cewar alkalin, an same Nwabuoku da laifi a dukkannin tuhume-tuhume guda tara da ake yi masa.
Saboda haka, kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru takwas a kan kowanne laifi, wanda idan aka hada ya kai shekaru 72.
Yadda kotu ta yanke hukunci
Sai dai kuma alkalin ya umarci cewa hukuncin zai gudana ne a lokaci guda, ma’ana ba lallai ne ya shafe dukkannin shekaru 72 a jere ba.

Source: Facebook
Alkalin ya kara da cewa:
“An same wanda ake kara da laifi kamar yadda aka tuhume shi."
Kotun ta bayyana cewa laifin da Nwabuoku ya aikata yana da muni matuka, musamman ganin cewa ya karkatar da kudaden da aka ware domin harkokin tsaro da kare kasa.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Tinubu ya tsallake rijiya, an gano wani mugun shiri da sojoji suka yi na kwace Aso Rock
An tabbatar da cewa ya kwashi kudin ne a lokacin da yake rike da mukamin Daraktan Kudi da Asusun Ma’aikatar Tsaro tsakanin shekarun 2019 zuwa 2021.
Alkalin ya bayyana wannan aiki a matsayin abin takaici matuka, yana mai yabawa EFCC bisa yadda ta gudanar da bincike da kuma gabatar da shaidu dalla-dalla.
Har ila yau, kotun ta lura cewa shaidar shaida ta tara da masu gabatar da kara suka kawo, wadda ta nuna cewa wanda ake kara ya mayar da wani bangare na kudin da aka karkatar.
Shaidan ya bayyana cewa an mayar da kudin da suka haura Naira miliyan 200 yayin bincike, kuma ba a musanta ta daga bangaren wanda aka tuhuma ba.
An kai Akanta Janar kotu
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta sake gurfanar da Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Jaja, tare da wasu da ake zargi da karkatar da kudin jama'a a gaban kotu.
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki ta'annati tana zargin Jaja da hada kai da wasu wajen aika Naira biliyan 1.48 zuwa asusun wani kamfani da ake zargin hada baki aka yi da shi.
Yanzu haka, hukumar tarayyar na neman karin wasu mutum uku da ake zargi da aikata laifuffuka da dama da suka hada da halasta kudin haram domin a gurfanar da su a gaban kotu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
