'Yan Ta'adda Sun Tashi Bam a Neja, Sun Datse Hanyar Kasuwancin Najeriya da Benin

'Yan Ta'adda Sun Tashi Bam a Neja, Sun Datse Hanyar Kasuwancin Najeriya da Benin

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun yi amfani da bam wajen tarwatsa wata gada mai muhimmanci a hanyar Wawa zuwa Guffanti a jihar Neja
  • Wannan harin ya datse hanyar kasuwanci da ta hada Najeriya da kasar Benin kwana daya kafin ranar kasuwar Babanna a yau Litinin
  • Mazauna yankin sun koka kan yadda wannan barna za ta jefa su cikin talauci sakamakon yanke hanyoyin kai kayan amfanin gona kasuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - 'Yan ta'adda da ake zargin 'yan Boko Haram ne ƙarƙashin jagorancin wani kwamanda mai suna Mallam Sadiku, sun tarwatsa wata gada da ta haɗa garuruwan jihar Neja da Jamhuriyyar Benin ta hanyar amfani da bam.

Wannan gagarumin hari ya afku ne a yammacin ranar Lahadi, 22 ga Maris, 2026, a kan hanyar Wawa zuwa Luma zuwa Guffanti.

Kara karanta wannan

Yakin Amurka, Isra'ila da Iran ya taba Najeriya, farashin litar fetur ya haura N1350

'Yan ta'adda sun yi amfani da bam sun tarwatsa wata muhimmiyar gada a Neja.
Taswirar jihar Neja, inda 'yan ta'adda suka tarwatsa wata muhimmiyar gada da bam. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan ta'adda sun tarwatsa gada a Neja

Wannan hanya, wadda ta kasance mai cike da hada-hadar mutane da ababen hawa, ta ratsa har ta cikin dajin Kainji Lake National Park, a cewar rahoton jaridar Premium Times.

Wannan daji ya zama matattarar ƙungiyoyin jihadi guda biyu; Ansaru (ko Mamuda) da kuma Boko Haram, waɗanda suka kafa sansanoninsu a wurin tsawon shekaru.

Mazauna yankin sun bayyana cewa wannan harin da ya tarwatsa gadar ya nuna ƙudurin 'yan ta'addan na durƙusar da tattalin arziƙin jama'ar da ke rayuwa a garuruwan wajen.

Tasirin tarwatsa gadar da kasuwanci a Neja

Mazauna garin Wawa sun bayyana wa manema labarai cewa 'yan ta'addan sun nuna tsantsar muguntarsu la'akari da lokacin da suka zaɓi kai harin

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa:

"Wannan harin ya faru ne kwana ɗaya kafin ranar kasuwar Babanna."

Wani direban mota mai suna Ahmed Yusuf, wanda ke ɗaukar 'yan kasuwa zuwa Babanna a safiyar Litinin, ya tabbatar da cewa hanyar ta yanke gaba ɗaya, inda ya ce motoci ba za su iya wucewa ba domin gadar ta dare gida biyu.

Kara karanta wannan

Ana ruguntsumin Sallah, 'yan bindiga sun kai hari, an sace masu ibada

A halin yanzu, masu amfani da babura ne kawai ke samun damar lallabawa ta cikin baraguzan gadar domin wucewa.

Abu Fudail, mazaunin garin New Bussa, ya wallafa bidiyon gadar da aka lalata a shafinsa na Facebook, inda ya yi gargaɗin cewa wannan wani yunƙuri ne na ƙara jefa talakawan yankin cikin talauci.

Kalli bidiyon a kasa:

Hanyar da ta haɗa Najeriya da Benin

Muhimmancin wannan hanya ya wuce yadda ake tsammani, domin 90% na manyan kasuwannin yankin ana samun damar isa gare su ne ta wannan hanyar.

Yadda 'yan ta'adda suka tarwatsa gadar Neja da bam
Gadar Neja da 'yan ta'adda suka tarwatsa ta hanyar amfani da bam. Hoto: Abu Fudail
Source: Facebook

Baya ga haɗa garuruwan jihar Neja, hanyar tana kaiwa har zuwa jihar Kebbi da Kontagora ta hanyar kogin Neja, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Mafi mahimmanci ma, hanyar tana haɗa garin Babanna da Jamhuriyyar Benin, wanda hakan ke nufin harin ya datse harkokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.

Wannan sabon harin ya sake tayar da fargaba kan tsaron yankin Borgu da kewayensa, musamman duba da yadda 'yan ta'adda ke ƙoƙarin mamaye dajin Kainji domin gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Iran ta yi babban rashi a ranar Sallah, kakakin rundunar IRGC ya mutu a harin Isra'ila

Mabuyar 'yan ta'adda a jihar Neja

A wani labari, mun ruwaito cewa, Majalisar dattawar Najeriya ta ce an gano mabuyar yan ta'adda a kananan hukumomi uku a jihohin Kwara da Niger.

Wannan na cikin batutuwan da aka tattauna a majalisar kan tabarbarewar tsaro a Kainji Lake National Park da garuruwa da ke kananan hukumomin Kaima, Baruten da Borgu a Jihar Niger.

A cewar majalisar, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka sun zama ruwan dare a garuruwan da ke kusa da Kainji Lake National Park kuma hakan ya saka tsoro a zukatan mutanen garuruwan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com