Barka: An kammala yashe kogin Neja, jiragen ruwa zasu fara shigowa Arewacin Najeriya

Barka: An kammala yashe kogin Neja, jiragen ruwa zasu fara shigowa Arewacin Najeriya

A watan gobe, wato watan Agusta ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabuwar tashar jirgin ruwa na zamani dake garin Baro, cikin karamar hukumar Agaie ta jihar Neja, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Shugaban hukumar hanyoyin ruwa na cikin gida, NIWA, Alhaji Danladi Ibrahim ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 18 ga watan Yuli, inda yace aikin yashe kogin Neja, tare da aikin tashar jiragen ruwan Baro yazo karshe, kuma a watan Agusta za’a kaddamar da fara aikinsa.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ya yi awon gaba da wata Amarya zuwa Nijar daga Katsina

“An gama aiki a tashar jirgin ruwa na Baro, a yanzu ana sanya na’urorin daukar kaya ne, muna sa ran zuwa watan gobe komai zai kammala, kuma za’a kaddamar da shi, haka zalika za’a kammala aikin mika tashar jirgin ruwa ta garin Onitsha gay an kasuwa a watan Agusta.

“An kwashe sama da shekaru uku ana aikin Baro, amma da zarar an kaddamar da fara aikinsa a wata mai zuwa zai fara samar da ayyuka ga matasa, da zasu kai miliyan biyu. Za’a dinga kwasar kaya zuwa yankunan Arewa maso yamma, da ta tsakiya, haka zalika an hada tashar da titin jirgin kasa.

“Itama tashar Onitsha zata inganta kasuwanci a yankin kudu maso gabashin kasarnan, a takaice ma tashar Onitsha sai ta fi hadahada, sakamakon kasha sittin na kayayyakin da ake shigowa dasu ta ruwa Onistsha ake kaisu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng