An Gano Mabuyar Yan Ta'adda A Jihohin Niger Da Kwara, Majalisar Dattawar Najeriya

An Gano Mabuyar Yan Ta'adda A Jihohin Niger Da Kwara, Majalisar Dattawar Najeriya

  • Majalisar Dattawar Najeriya ta bayyana cewa an gano mabuyar yan ta'adda a wasu kananan hukumomi a jihohin Niger da Kwara
  • Sanata Sadiq Umar ne ya bayyana hakan cikin wata kudiri da ya gabatar a gaban majalisar yana mai cewa abin ya shafi kananan hukumomin Kaima, Baruten da Borgu a Jihar Niger
  • Majalisar ta umurci rundunar sojojin Najeriya ta gudanar da atisaye a yankunan da abin ya shafa da nufin kawar da yan ta'addan da suke adabar mutane

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT Abuja - Majalisar Dattawar Najeriya ta ce an gano mabuyar yan ta'adda a kananan hukumomi uku a jihohin Kwara da Niger, rahoton Channels Television.

Wannan na cikin batutuwan da aka tattauna a majalisar bayan wani sanata ya gabatar da kudiri kan tabarbarewar tsaro a Kainji Lake National Parki da garuruwa da ke kananan hukumomin Kaima, Baruten da Borgu a Jihar Niger.

Kara karanta wannan

Daya daga 'yan matan Chibok: Na san marigayi Shekau, sauran mata 20 a hannun BH

Majalisar Dokokin Najeriya.
An Gano Mabuyar Yan Ta'adda A Jihohin Niger Da Kwara, Majalisar Dattawar Najeriya. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar wanda ya gabatar da kudirin, Sanata Sadiq Umar, garkuwa da mutane da sauran laifuka sun zama ruwan dare a garuruwan da ke kusa da Kainji Lake National Park kuma hakan ya saka tsoro a zukatan mutanen garuruwan.

"Mutane da dama suna barin kauyukansu da gonakinsu suna neman mafaka a birane da nan gaba suma za su fuskanci barazana idan ba a dauki mataki kan matsalar tsaron ba. Wasu garuruwan ma sun fara biyan bata garin wani nau'in haraji domin su kyalle su su zauna lafiya," in ji Umar.

Majalisar, don haka, ta bukaci rundunar sojojin Najeriya ta shirya atisaye na musamman don kawar da yan ta'adda da wasu bata gari a yankin na Kainji Lake National Park da garuruwan da ke kewayensa.

Dogo Nabajallah: Ƙasurgumin Ɗan Bindigan Katsina Ya Gamu Da Ajalinsa Sakamakon Rikicin Neman Aure

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 85, Buhari ya ce lokacin ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya yi

A wani labarin daban, rikici ya barke tsakanin bangarorin ƴan bindiga biyu masu adawa da juna a Katsina wadda ya yi sanadin mutuwar shugaban yan bindiga, Nabajallah, da wasu yan bindigan uku, rahoton The Punch.

Majiyoyi sun ce an kashe shugaban yan bindiga, Dogo Nabajallah a cikin dajin Dungun Muazu da ke karamar hukumar Sabuwa a ranar Laraba.

A cewar rahoton Premium Times Hausa wasu ƴan bindigan da ke adawa da shi ne suka afka masa suka kashe shi saboda rikicin neman aure da ke tsakanin yaronsa da bangaren su yan adawan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel