Bala’in da ke Tunkaro Najeriya da Kasashen Afirka kan Yakin Iran da Isra’ila
- Hukumar kula da abinci ta duniya ta yi gargadin cewa mutane miliyan 10.4 a Yammaci da Tsakiyar Afirka na iya fuskantar yunwa
- Rikicin Iran da isra’ila tare da Amurka na iya haddasa matsalar abinci a duniya wanda har yanzu ake ci gaba da yi
- Har ila yau, kungiyar inganta noma da abinci ta ce kasashe 31 a Afirka na bukatar tallafin abinci ciki har da Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar kula da abinci ta duniya ta yi gargadin halin da za a shiga na yunwa a Najeriya da wasu kasashen Nahiyar Afirka.
Hukumar ta bayyana cewa kimanin mutane miliyan 10.4 a Yammaci da Tsakiyar Afirka na iya fadawa cikin matsananciyar yunwa idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ci gaba.

Source: Facebook
Rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa rikicin da ya hada da Iran da kuma hadin gwiwar isra’ila da Amurka na iya jefa duniya cikin matsalar abinci, cewar The Guardian.
Matsalar da yakin Iran/Isra'ila ya jawo
Hakan ya biyo bayan barkewar yaki tsakanin Iran da Isra'ila tun a ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 da muke ciki.
Yakin ya jawo hauhawar farashin man fetur a duniya da kuma wasu kayayyakin masarufi da ake amfani da su.
Shugaba Donald Trump ya ce man fetur zai sauka da zarar an kammala yakin da ake yi ba tare da bata lkaci ba.

Source: Getty Images
Gargadi kan fadawa yunwa a nahiyar Afirka
Hukumar ta ce karin mutane miliyan 45 na iya fadawa cikin yunwa a duniya, wanda zai karu kan miliyan 318 da ke fama da yunwa a yanzu.
A cewar Carl Skau, idan rikicin ya ci gaba, zai girgiza duniya kuma zai kara jefa talakawa cikin wahala.
Ya ce rashin isasshen tallafin jin kai na iya janyo bala’i ga miliyoyin mutane da ke rayuwa cikin kunci.
Hukumar ta kuma bayyana cewa kasashen Afirka da suka dogara da shigo da abinci da mai za su fi fuskantar matsalar abinci.
Rahoton ya nuna cewa adadin masu fama da yunwa zai karu da kashi 21 cikin 100 a Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Haka kuma, zai karu da kashi 17 cikin 100 a Gabas da Kudancin Afirka idan farashin mai ya ci gaba da tsada, cewar rahoton Nairametrics.
A nata bangaren, hukumar inganta abinci da noma ta ce kasashe 41 a duniya na bukatar tallafin abinci, ciki har da 31 a Afirka.
Kasashen Afirka da dama ciki har da Najeriya na fuskantar matsaloli sakamakon rikice-rikice, sauyin yanayi da tsadar kayayyaki.
Yadda yakin Iran da Isra'ila zai taimaki Najeriya
A wani labarin, 'dan siyasa kuma attajiri, Jimoh Ibrahim ya yi magana kan yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.
'Dan majalisar ya ce rikicin Gabas ta Tsakiya na iya zama dama ga Najeriya saboda karin kudin man fetur zai iya karfafa Naira tare da rage karbar bashi.
Sanatan ya kuma yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da bashi, yana cewa halin tattalin arzikin kasar na kara inganta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

