Ana Jiran Hukuncin Babbar Shari'ar da Za Ta Bayyana Makomar Jam'iyyar PDP
- Jam'iyyar PDP na ci gaba da samun kanta cikin rikicin shugabanci wanda ya ki ci ya ki cinyewa har na tsawon lokaci
- Bangarorin da ke ikirarin shugabancin jam'iyyar sun shigar da kararraki a gaban kotu inda suke jiran yanke hukunci
- Kotun daukaka kara ta shirya yanke hukunci kan kararrakin da ke gabanta wadanda suka shafi rikicin shugabancin jam'iyyar PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Bangarorin da ke rigima kan shugabancin jam'iyyar PDP sun nuna kwarin gwiwar yin nasara a gaban kotu.
Bangaren da ke samun goyon bayan gwamnonin PDP da wanda ke biyayya ga Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, sun nuna kwarin gwiwar cewa hukuncin kotu zai yi musu dadi.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam'iyyar PDP a ranar Litinin, 9 ga watan Maris 2026.
Bangarorin PDP na da kwarin gwiwa
Sakataren yaɗa labarai na kasa na kwamitin (NWC) ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki (SAN), wanda Gwamna Seyi Makinde da Bala Mohammed goyon baya, Ini Ememobong, ya tabbatar da cewa kotun ta sanya yau Litinin domin yanke hukunci kan kararraki daban-daban da aka haɗe waje ɗaya.
Haka zalika, sakataren yaɗa labarai na kwamitin riƙon ƙarya karlashin Mohammed Abdulrahman da Samuel Anyanwu, waɗanda Wike ke goyon baya, Jungudo Mohammed, ya tabbatar da cewa an sanya ranar yau domin yanke hukunci kan takaddamar shugabancin a Abuja.
Tushen rikicin shugabancin jam'iyyar PDP
Gwamnonin PDP sun amince da babban taron Ibadan wanda ya samar da Turaki a matsayin shugaban NWC ranar 15 ga Nuwamban 2025 na tsawon shekaru huɗu.
Gwamnonin sun kuma jagoranci miƙa mulki daga tsohon shugaban riƙon ƙarya, Umar Damagum, zuwa ga Turaki kafin wa’adin Damagum ya ƙare ranar 9 ga Disamban 2025.
A ɗaya ɓangaren kuma, bangaren da ke biyayya ga Ministan Abuja sun kafa kwamitin riƙon ƙarya na mutane 13 ranar 8 ga Disamban 2025, inda suka naɗa Abdulrahman a matsayin shugaban riƙon ƙarya na tsawon kwanaki 60.
Rufe sakatariyar Wadata Plaza
Ƙoƙarin ɓangarorin biyu na gudanar da taro a sakatariyar jam’iyyar ranar 18 ga Nuwamban 2205, 2025, ya juye zuwa hargitsi da faɗace-faɗace.
Wannan ya sa rundunar 'yan sandan Najeriya ta rufe sakatariyar har zuwa yau. Hukumar INEC kuma ta ƙi amincewa da kowane ɓangare, wanda hakan ya kai ga kwashe lokaci ana dambarwar shari'a.
Muhimman Kararrakin da ke gaban kotu
Daga cikin ƙararrakin da aka haɗe akwai mai lamba FHC/ABJ/CS/2120/2025, wadda ta dakatar da babban taron jam’iyyar har sai an bi ƙa’idojin kundin tsarin mulkin jam’iyyar da na Najeriya.
Shari’ar Sule Lamido inda mai shari'a Peter Lifu ya bayar da umarnin hana INEC sanya ido ko amincewa da kowane taron PDP da ya cire mai shigar karar zama a matsayin ɗan takara.

Source: Twitter
Akwai shari'a mai lamba FHC/ABJ/CS/2520/2025 kan rufe sakatariyar jam’iyyar da aka shigar a kan rundunar 'yan sanda.
Hakazalika, akwai kuma wasu kararraki uku ciki har da wadda ta fito daga babbar kotun jihar Oyo, wadanda ke kalubalantar sahihancin babban taron PDP ta fuskar doka.
A ranar 12 ga Fabrairun 2026, kotun daukaka kara ta saurari dukkan waɗannan ƙararrakin, kuma a makon jiya ta sanar da ɓangarorin cewa za a yanke hukunci a yau Litinin.
Sanata ya fice daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Seriake Dickson wanda ke wakiltar Bayelsa ta Yamma a majalisar dattawa, ya fice daga jam'iyyar PDP.
Sanata Seriake Dickson ya kuma sanar da sauya sheƙa daga PDP zuwa sabuwar jam’iyyar NDC da INEC ta yi wa rijista.
Tsohon gwamnan ya nuna damuwa kan halin da PDP ta tsinci kanta, yana cewa jam’iyyar da ta taba kawo farin ciki ga magoya bayansa ta zama mai tsananin rauni.
Asali: Legit.ng


