ICPC Ta Gano Wasu Gidajen Alfarma da ake Zargin El Rufai Ya Mallaka a Ƙasar Waje

ICPC Ta Gano Wasu Gidajen Alfarma da ake Zargin El Rufai Ya Mallaka a Ƙasar Waje

  • Hukumar ICPC ta gano wasu manyan kadarori a ƙasar Masar da ake zargin suna da alaƙa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
  • Rahotanni sun nuna cewa an sayi kadarorin ne tsakanin shekarun 2021 zuwa 2023 a wasu unguwanni masu tsada na New Cairo
  • Ana binciken gidaje da gidajen haya da dama a wurare irin su Arabella Estate, Banafsek Estate, Oriana Estate da Cairo Festival City

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Masu bincike na hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) sun gano wasu manyan kadarori a ƙasar Masar da ake zargin suna da alaƙa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Jami’an da ke da masaniya kan binciken sun bayyana cewa ana zargin an sayi kadarorin masu darajar biliyoyin Naira tsakanin shekarun 2021 zuwa 2023.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da yaki da Iran, an jefa abubuwan fashewa a kasar Amurka

An fara bibiyar kadarorin El-Rufa'i
Tsohon gwamnan Kaduna da ke hannun ICPC Nasir El-Ryfa'i Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

Labarin da ya kebanta ga Daily Nigerian ya ce wasu majiyoyi daga cikin hukumar yaki da rashawar, wadanda suka nemi a sakaya sunansu ne suka tabbatar da lamarin.

Ana binciken alakar El-Rufa'i da kadarori a Masar

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa majiyoyin sun ce kadarorin da ake zargin El-Rufa'i ya mallaka suna cikin wasu unguwanni masu matuƙar tsada a New Cairo.

Wannan yanki na New Cairo ya shahara da gidajen alfarma da kuma gidaje masu katanga da tsaro mai ƙarfi.

Binciken ya nuna cewa akwai wasu tafka-tafkan gidajen haya da dama a yankin da ake zargin suna da alaƙa da tsohon gwamnan.

Rahotanni sun ce kadarorin suna cikin manyan rukunin gidaje da suka hada da Arabella Estate, Banafsek Estate, Oriana Estate da kuma Cairo Festival City.

Darajar kadarorin da ake zargin El-Rufa'i ya mallaka

Bayanan da aka samu sun nuna cewa farashin kowane babban gida a wuraren Cairo Festival City da Arabella na kaiwa tsakanin Fam miliyan 50 zuwa miliyan 200 na Masar, wanda ya kai kusan Naira biliyan 5.3.

Kara karanta wannan

Martanin malaman addini 5 game da yaƙin Iran da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya

A bangaren gidajen haya kuwa, ana sayar da su kusan Fam miliyan 26 na Masar, wanda ya kai kusan Naira miliyan 700.

Wani jami’i da ke cikin binciken ya bayyana cewa daga cikin kadarorin da ake dubawa akwai wani babban gida da ke da lamba 113 a Arabella Estate a yankin Fifth Settlement na New Cairo.

Haka kuma ana zargin wani makeken gidan na nan a lamba18 a Banafsek Estate a yankin First Settlement yana da alaƙa da tsohon gwamnan.

Ana zargin El-Rufa'i ya mallaki manyan gidajen alfarma a Cairo
Malam Nasir El-Rufai tsohon gwamnan Kaduna Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Masu binciken sun kuma ambaci wani gida a Oriana II Estate, kusa da Jam'iar Amurka a Cairo, wanda aka bayyana gida mai lamba 11.

Baya ga manyan gidajen, an kuma gano wasu gidajen haya a babban rukunin gidaje na Cairo Festival City.

Majiyoyin sun ce gidaje hudu da aka bayyana da lambobin 514, 515, 516 da 517 na daga cikin kadarorin da ake bincike a kansu.

Har ila yau, akwai wasu gidaje biyu a Oriana Estate masu lambobin 4000 da 4100 da ake dubawa a matsayin wani bangare na bincike.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya

El-Rufa'i ya kinkimo babban aiki

A baya, mun wallafa cewa ana ci gaba da musayar yawu tsakanin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da hukumar yaki da cin hanci mai zaman kanta ta ICPC.

Tsohon gwamnan, Malam El-Rufai da iyalansa sun mika bukatunsu ga hukumar ICPC kan wasu zarge-zarge da ta yi a kan tsohon gwamnan, inda suka bayyana su da bita-da-kulli.

El-Rufai da iyalansa sun buƙaci biyan diyar kuɗi har Naira biliyan 15.6 daga ICPC sakamakon kama shi, tsare shi, da kuma bayanan ƙarya da aka fitar a kansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng