Magana Ta Fito: An Ji 'dalilin' da Ya Sa Tinubu Ya Hana El Rufai Mukamin Minista

Magana Ta Fito: An Ji 'dalilin' da Ya Sa Tinubu Ya Hana El Rufai Mukamin Minista

  • Tsohon ministan sufurin jiragen sama a Najeriya, Femi Fani-Kayode ya yi magana game da dalilin hana Nasir El-Rufai mukamin minista
  • Tsohon ministan ya ce zarge-zargen cewa wasu manyan jami’an gwamnati sun shirya makarkashiya domin hana El-Rufai mukamin minista karya ne
  • Fani-Kayode ya kuma zargi El-Rufai da aikata rusau da take hakkin jama’a lokacin da yake ministan Abuja da kuma gwamnan Kaduna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jakadan Najeriya da aka nada zuwa Germany, Femi Fani-Kayode ya bayyana abin da ya haddasa kin amincewa da nadin Nasir El-Rufai a matsayin minista.

Ya ce sabanin abin da ake yadawa, ba wata makarkashiya daga wasu manyan jami’an gwamnati ba ce ta hana El-Rufai zama minista.

An 'gano' dalilin hana El-Rufai mukamin minista
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da Bola Tinubu. Hoto: Nasir El-Rufai, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Fani-Kayode ya caccaki Nasir El-Rufai

A cikin rubutunsa da ya wallafa a Facebook, ya ce kungiyoyin Musulmi na Shi’a da Tijjaniyya da kuma Kiristoci a Kaduna sun gabatar da koke-koke kan zargin take hakkinsu a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

"Kada a dagula siyasar Kano": NNPP ta aika sako kan shirin tsige Mataimakin gwamna

Fani-Kayode ya ce wadannan koke-koken sun isa hannun jami’an tsaro lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya mika sunan El-Rufai domin mukamin minista.

Ya kara da cewa koke-koken sun kasance masu tsanani sosai har Majalisar Dattawa ta kasa yin watsi da su, lamarin da ya sa aka ki amincewa da nadin.

Tsohon ministan ya kuma zargi El-Rufai da rushe gidaje da cibiyoyi da dama, ciki har da gidajen marayu, lokacin da yake jagorantar gwamnati.

A cewarsa, irin wadannan matakai da ya ce sun cutar da jama’a ne suka jawo matsalolin siyasa da shari’a da tsohon gwamnan ke fuskanta yanzu.

Ya ce:

“Wadannan koke-koke sun kasance masu tayar da hankali matuka har ba za a iya yin watsi da su ba, shi ya sa Majalisar Dattawa ta ki amincewa da nadinsa a matsayin minista.
“Idan da Shugaba Tinubu bai so ya zama minista ba tun farko, da ma ba zai mika sunansa domin nadin ba.”
Tsohon minista ya tona dalilin hana El-Rufai mukamin minista
Tsohon minista a Najeriya, Femi Fani-Kayode. Hoto: Femi Fani-Kayode.
Source: Twitter

Zarge-zargen da ake yiwa El-Rufai

Fani-Kayode ya zargi Nasir El-Rufai da rusa gidajen marayu da dama, lamarin da ya sa marayu da yawa suka rasa matsuguni.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani kan jita jitar kashe wanda ake sa ran zai gaji Khamenei a Iran

Baya ga haka, ya ce El-Rufai ya rusa gidaje da gine-gine kusan 2,000 a Abuja, sannan ya rusa kusan bukkoki 12,000 a wajen birnin, inda talakawa suka samu mafaka — sau da yawa ba tare da bin umarnin kotu ba kuma ba tare da biyan diyya ba.

Ya ce:

“Na kuma manta in ambaci cewa ya rusa gidajen marayu da dama a Kaduna lokacin da yake gwamna.
Har ila yau, daya daga cikin abubuwan karshe da ya yi kafin barin mulki, wanda ya aiwatar cikin rashin tausayi da sanyi a ranar da ta gabaci mika mulki ga Uba Sani, shi ne rusa wani gidan marayu a Fadama Badan Dodo a Zaria.”

Dan El-Rufai ya magantu kan cafke mahaifinsa

An ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta ce ta gano nau'rorin yin kutse ta waya a gidan Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Dan tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Mohammed Bello El-Rufai, ya fito ya yi magana kan zarge-zargen da ICPC ke yi wa mahaifinsa.

Bello El-Rufai ya bayyana cewa hukumar tana son yin amfani ne da shirun da mahaifinsa ya yi a matsayin makamin da za ta yi yaki a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.