Gbajabiamila da Sauran Yaran Tinubu da Suka Rike Amana Yau ake Damawa da su a Gwamnati

Gbajabiamila da Sauran Yaran Tinubu da Suka Rike Amana Yau ake Damawa da su a Gwamnati

Shekaru fiye da 30 da suka wuce Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya shiga siyasa kuma yake da wasu yara da ya kasance tare da su na tsawon shekara da shekaru.

Sabon nadin da aka yi wa shugaban Kwamitin Shugaban kasa kan manufofin kudi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele, a matsayin Karamin Ministan Kudi ya tado zancen nan.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Nadin Taiwo Oyedele ya fara jawo hasashen cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana kara kaimi wajen kara karfafa kusoshinsa na siyasa gabanin zaben 2027.

Yanzu haka shugaban kasar ya shafe kusan shekaru uku a wa’adinsa na farko, kuma alamu sun nuna cewa ana sake tsara nade-nade da siyasarsa gabanin 2027 da ke matsowa.

Kara karanta wannan

Dalilin gidan gyaran hali na cigaba da tsare Abba Kyari duk da hukuncin kotu

Shugaba Tinubu ya kewaye kansa da makusantansa
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa majiyoyi sun ce abin da ke faruwa a fadar shugaban kasa ba sabon abu ba ne, domin an dade ana sanin Tinubu da dabi’ar kewaye kansa da abokan siyasa da ya aminta da su.

Bola Tinubu ya yi sababbin nade-nade

Jaridar Punch ta wallafa cewa a ranar Juma’a 6 ga watan Maris, 2026, Fadar shugaban kasa ta sanar da nada jakadu, inda rahotanni suka nuna cewa an yi ta fafutukar neman mukaman kafin a tabbatar da su.

Bayan wadannan nade-nade, an kuma sanar da nadin Taiwo Oyedele, wanda ya zo jim kadan bayan nada sabon Sufeton yan sanda, Tunji Disu.

Na hannun daman Tinubu da ke gwamnati

Daga cikin wadanda ake ganin suna kusa da shugaban akwai Ministan Kudi Wale Edun da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Yemi Cardoso.

Jerin wadanda ke da kusancin da Shugaban a gwamnati sun hada da:

1. Femi Gbajabiamila

Kara karanta wannan

Aminu Gwarzo: Matakai 8 da majalisar Kano za ta bi don tsige mataimakin gwamna

A tsawon shekaru, Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shi ne Shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban kasa ya zama daya daga cikin fitattun mutane da ke tare da Bola Ahmed Tinubu.

Gbajabiamila na daga cikin makusantan Tinubu
Femi Gbadabiamila tare da Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tafiyarsa ta siyasa na nuna yadda tsarin siyasar da Tinubu ya gina sama da shekaru 20 ya samar da gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa da shugabannin jam’iyya a sassa daban-daban na Najeriya.

Daukakar Gbajabiamila a siyasa ta fara ne a lokacin da ya zama 'dan majalisar wakilai a lokacin Tinubu yana gwamna a jihar Legas.

Shi lauya ne da ya yi aiki a Amurka kafin ya dawo Najeriya. Ya shiga siyasa a farkon shekarun 2000, inda aka zabe shi a Majalisar Wakilai a 2003 yana wakiltar mazabar Surulere.

2. Hakeem Muri-Okunola

A cikin masu taimaka wa Tinubu da ya amince da su, kuma ya yi sa'a tasirinsa na karuwa shi ne Hakeem Muri-Okunola, wanda ake kira da “HMO”.

Ya taba zama shugaban ma’aikatan gwamnatin Legas tun yana matashi, lamarin da ya nuna irin saurin daukakar da ya samu a harkar gwamnati.

Hakeem Muri Okunola ya shiga jerin makusantan Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, Hakeem Muri-Okunola Hoto: Hakeem Muri -Okunola Support group
Source: Facebook

An ce dangantakar da ke tsakanin Tinubu da iyalinsu ta sa shugaban kasar ke kallonsa kamar dan gida. An nada shi Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Legas a 2019 ta hannun Gwamna Babajide Sanwo-Olu.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar tsohon ministan Tinubu ya yake shi, yana kus kus da kusoshin adawa

Bayan Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023, an nada shi babban Sakataren Shugaban Kasa. Yanzu haka ana ganin shi a matsayin daya daga cikin masu yiwuwar takarar gwamnan Legas a 2027.

3. Wale Edun

Wale Edun na daga cikin manyan kwararru da Tinubu ya dade yana amincewa da su. Dangantakarsu ta fara tun lokacin da Shugaban yake gwamnan Legas a tsakanin 1999 zuwa 2007.

A lokacin, Edun ya kasance Kwamishinan kudi, inda ya taka rawa wajen aiwatar da sauye-sauyen tsarin kudi da suka zama abin koyi ga sauran jihohi.

Tinubu ya tafi da Wale Edun tun yana gwamna
Ministan kudi Wale Edun, Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto; Wale Edun/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kuma jagoranci tawagar masu ba da shawara kan tattalin arziki a lokacin yakin neman zaben Tinubu na 2023.

Bayan Tinubu ya hau mulki, an fara nada shi mai ba shugaban kasa shawara kan manufofin kudi, daga baya kuma ya zama Ministan ma'aikatar kudi kuma mai kula da tattalin arziki.

Ko da yake akwai jita-jita na sabani tsakaninsa da wasu a cikin tawagar tattalin arziki, har yanzu ana kallonsa a matsayin muhimmin mutum a cikin tsarin gwamnatin Tinubu.

4. Mudashiru Obasa

Yadda Mudashiru Obasa a rika buga Legas na daya daga cikin misalan aminci da dabarun siyasa a karkashin Tinubu.

Kara karanta wannan

An yi yunkurin hallaka Tinubu ta hanyar sanya masa guba a abinci? Gaskiya ta fito

Ya fara daga siyasar unguwa a Agege, wuri da aka dade ana saninsa da karfin siyasa a Legas.

Mushairu Obasa na daga cikin na hannun daman Tinubu da ke gwamnatin Legas a yanzu
Kakakin majalisar Legas, Rt Hon Mudashiru Obasa Hoto; Hon Mudashiru Obasa
Source: Facebook

A tsawon shekaru 10 da suka gabata, ya kasance shugaban majalisar dokokin Legas. Yunkurin tsige shi da aka yi a 2025 bai yi nasara ba.

Kafin ya zama Kakakin Majalisar dokokin Legas, ya shahara wajen samun goyon bayan jama’a a matakin kasa-kasa.

Wannan ya sa ya zama daya daga cikin muhimman ginshikan tsarin siyasar Tinubu inda ake ganin zai taka rawa a siyasar Shugaban kasa.

5. Taiwo Oyedele

Taiwo Oyedele ya shahara sosai a cikin da’irar shugaban kasa ba sai bayan zaben 2023, kuma a jiya 6 ga watan Maris, 2026 an kara daga likkafarsa.

Tinubu ya daga likkafar Taiwo Oyedele
Taiwo Oyedele tare da Bola Tinubu Hoto; @aonanuga1956
Source: Twitter

Kwararre ne a harkar haraji, kudi da manufofin gwamnati. Ya taba aiki a manyan kamfanonin ba da shawara na duniya kamar PricewaterhouseCoopers (PwC).

Kwamitinsa ya tsara dokokin haraji guda hudu da aka amince da su domin gyara tsarin haraji na Najeriya.

6. Olayemi Cardoso

Olayemi Cardoso shi ne gwamnan babban bankn Najeriya. An nada shi bayan Tinubu ya hau mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Jagoran Musulunci na Iran: Mutane 5 da za su iya maye gurbin Ayotallah Khamenei

Tinubu ya nada Cardoso a matsayin gwamnan babban bankin kasa
Olayemi Cardoso, Shugaban CBN a Najeriya Hoto: CBN
Source: Twitter

Kwararren ma'aikacin banki ne kuma masanin tattalin arziki, kuma yana da gogewa a bangarori masu zaman kansu da gwamnati.

Yana taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin kudi, da kokarin daidaita darajar naira da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.

7. Adegboyega Oyetola

Adegboyega Oyetola na daga cikin amintattun abokan Tinubu. Ya taba zama gwamnan Osun State tsakanin 2018 zuwa 2022 a karkashin APC.

Ana ganin yana da muhimmiyar rawa wajen karfafa tasirin shugaban kasa a yankin kudu maso yamma.

8. Zacch Adedeji

Zacch Adelabu Adedeji shi ne shugaban hukumar tattara kudin shiga a Najeriya. Ya taba zama Kwamishinan Kudi a jihar Oyo a lokacin marigayi Abiola Ajimobi.

Ana ganin yadda yake tafiyar da hukumar kudaden shiga ya kara masa karbuwa a wajen shugaban kasa.

9. Bayo Onanuga

A 2023, Tinubu ya nada Bayo Onanuga a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai.

Tun a lokacin mulkin soja ya yi aiki tare da Tinubu, kuma ya taba gudun hijira kafin ya dawo bayan mutuwar Sani Abacha.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci da suka yi wa Tinubu rubdugu da ya nemi gafarar 'yan Najeriya

10. Dele Alake

Dele Alake shi ne Ministan ma'adanan kasa. Ya taba zama Kwamishinan yada labaran gwamnatin Legas a lokacin Tinubu yana gwamna.

Da farko ya zama hadimi ne kafin a nada ministoci a Agustan 2023. Ana ganin yana taka rawa a bayan fage wajen shirin wa’adin mulki na biyu na shugaban kasa.

11. Nuhu Ribadu

Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, yana daga cikin na kusa da shugaban kasa musamman kan al’amuran tsaro da siyasar arewa.

Ana ganin Nuhu Ribadu na daga cikin makusantan Shugaban kasa
Mashawarcin Tinubu a kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Ya taba zama shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, kuma ana ganin zai taka muhimmayar rawa a zaben 2027 mai zuwa.

Babbar alakarsa tda Tinubu ita ce a 2011 lokacin da tsohon gwamnan ya ba shi damar tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyarsu ta ACN.

12. MC Oluomo

Musiliu Akinsanya ya taso daga shugabancin kungiyar direbobi zuwa daya daga cikin manyan masu hada jama’a a siyasa.

Kara karanta wannan

Ta zo gidan sauki: Tinubu ya fadi abin da za a tallata shi da shi a zaben 2027

Tasirin da yake da shi a cikin kungiyar direbobi a Legas ya taimaka wajen tara kuri’u ga APC a Legas.

Shugaba Tinubu ya tura jakadu waje

A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura jakadu kasashen Iran da Isra'ila yayin da suke cigaba da aika makamai masu linzami ga juna.

Mutanen da shugaban kasar ya tura na cikin jerin jakadu 63 da za su wakilci Najeriya a kasashe daban-daban bayan majalisa ta tantance su bayan shekaru kusan uku a mulki.

Daga cikin wadanda za su wakilci Najeriya a waje, Fadar shugaban kasa ta ce Salau Mohammed zai je Iran yayin da Nkechi Ufochukwu za ta tafi kasar Yahudawa ta Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng