Halin da Maniyyata ke Ciki yayin da Rikicin Iran da Isra’ila ke Kara Ta’azzara
- Rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila na iya jawo cikas ga tafiyar maniyyatan Umrah daga Najeriya
- Rufe wasu filayen jirgin sama a Gabas ta Tsakiya ya haddasa rudani da fargaba ga masu shirin zuwa Saudiyya
- Duk da cewa Saudiyya ba ta rufe filayen jiragen sama ba, ana tsoron hare-haren za su iya shafar jigilar maniyyata
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rikicin da ya kunno kai tsakanin Iran da hadin gwiwar Amurka da Isra’ila na iya yin tasiri kai tsaye kan tafiyar maniyyatan Umrah daga Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa yakin ya sa wasu kasashen Gabas ta Tsakiya rufe filayen jiragensu na wucin gadi, lamarin da ya kawo tsaiko ga harkokin sufurin jiragen sama.

Source: Facebook
Yadda rikicin Iran, Isra'ila zai iya shafar maniyyata
Wannan mataki ya shafi kamfanonin jiragen sama da ke jigilar matafiya da maniyyata zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da Umrah a watan Ramadan, cewar BBC Hausa.
A duk shekara, miliyoyin Musulmi kan yi tururuwa zuwa Saudiyya domin Umrah, inda kididdiga ta nuna cewa a 2025 kadai fiye da mutane miliyan 122 suka gudanar da ibadar.
Sai dai yanayin dar-dar da ake ciki a yankin ya haifar da rufe wasu muhimman hanyoyin jiragen sama da ake bi zuwa Saudiyya, abin da ya jefa maniyyatan Najeriya cikin rashin tabbas.
Kasashe irin su Iran da Iraq da Isra’ila da Syria da Kuwait da Qatar da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa sun sanar da rufe filayen jiragen sama na dan wani lokaci bayan hare-haren da aka kai kan Iran.

Kara karanta wannan
Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya saboda rikicin Isra'ila, Iran? an ji gaskiyar zance
Matakin ya haddasa tangarda mai tsanani a zirga-zirgar jiragen sama a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wannan lamari ya kara tayar da hankalin maniyyata daga Najeriya, wadanda ke fargabar ko za su samu damar sauke farali a wannan lokaci.

Source: Facebook
Wace matsaya hukumomin Saudiyya suka fitar?
Har zuwa yanzu, hukumomin Saudiyya ba su sanar da rufe filayen jiragen saman kasar ba duk da ci gaba da kai hare-hare da ake yi.
Duk da haka, akwai damuwa cewa idan rikicin ya kara tsananta, hakan na iya shafar zirga-zirga zuwa kasa mai tsarki, cewar The Nation.
Tun bayan barkewar rikicin, tafiye-tafiyen jiragen sama sun fuskanci kalubale mai yawa, lamarin da ya jawo tsaiko ga masu shirin tafiya ko dawowa daga Umrah.
A halin yanzu, babu tabbas kan yadda lamarin zai kaya idan hare-haren suka ci gaba a tsakanin bangarorin da ke rikici.
Wani daga cikin maniyyata da ke zuwa Umrah, Alhaji Zaharaddeen Abubakar ya ce fargabar su ba ta wuce yadda wasu sun riga sun kama ɗakuna kuma suna da duk takardun tafiya amma babu hali.
''Wanda ya ke Saudiyya kuma, ya gama aikin ibadar shi zai dawo, idan jiragen da ke can ba za su tashi ba, ka ga shi ma abin fargaba ne."
Alhaji Ibrahim Mohammed daga Gombe ya ce yana cikin fargaba saboda rashin sanin tabbas game da zuwa Umrah a bana domin ya shirya komai.
Fasto ya zaiyarci Makka da Madina
Kun ji cewa Fasto Israel Ogundipe ya yi magana bayan shan suka game da ziyarar da ya kai zuwa Makka da Madina a Saudiyya wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.
Fasto Israel Ogundipe ya kare ziyarar da ya kai biranen masu tsarki bayan suka a kafafen sada zumunta da zarge-zarge.
Malamin ya jaddada muhimmancin fahimtar juna da ‘yancin binciken addini a duniyar da ake da mabambantan addinai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


