Ana Yakin Iran da Amurka, 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Sojoji, Sun Yi Barna

Ana Yakin Iran da Amurka, 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Sojoji, Sun Yi Barna

  • Mayakan kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a jihar Borno kan wani sansanin dakarun sojojin Najeriya
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun kashe kwamandan sojoji na sansanin bayan an kwashe dogon lokaci ana musayar wuta tsakanin bangarorin biyu
  • Majiyoyi sun bayyana matsalar da aka samu wadda ta jawo kwamandan ya gaza fatattakar maharan duk kuwa da irin jarumtar da ya nuna yayin artabun

​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Mayakan kungiyar 'yan ta’addan Boko Haram sun kashe kwamandan sansanin sojoji na FOB wanda yake babban jami’i ne mai muƙamin Manjo.

'Yan ta'addan sun kuma kashe sojoji uku da kuma mafarauci ɗaya yayin wani mummunan hari da suka kai wa sansanin sojojin da ke Mayanti, a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.

'Yan Boko Haram sun kashe kwamandan sojoji a Borno
Shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Majiyoyin tsaro sun tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa an kashe jami’an ne yayin wani farmaki na haɗin gwiwa da ’yan ta’addan suka kai da daren Lahadi, 1 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta biya kudi kafin Amurka ta turo sojoji zuwa Najeriya? Hedkwatar tsaro ta yi bayani

Kwamandan sojoji ya nuna bajinta

A cewar wata majiya, kwamandan wanda aka bayyana sunansa da Manjo IU Mairiga, ya nuna jarumtaka sosai wajen fafatawa da maharan.

Sai dai, daga ƙarshe 'yan ta'addan sun samu rinjaye a kan shi bayan da wasu daga cikin dakarunsa suka gudu zuwa cikin daji, jaridar Sahara Reporters ta kawo labarin.

“Kwamandan ya fafata da ’yan ta’addan sosai, amma sun fi ƙarfinsa bayan wasu sojoji sun gudu. Ya mutu a matsayin jarumin soja kuma ya kashe da dama daga cikinsu kafin su yi nasara a kansa."

- Wata majiya

Sojoji sun gano makamai masu yawa

Ya ƙara da cewa bayan isowar dakarun kawo dauki, sojojin sun gano makaman harba roka (RPGs), bindigogin harbo jirage da bindigogi ƙirar PKT, yayin da aka ga gawarwakin ’yan ta’adda da dama a wurin.

“Ba don janyewar wasu daga cikin mutanensa ba, da ya yi nasarar fatattakar maharan."

- Wata majiya

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi kazamin fada da Boko Haram, an zubar da jinin 'yan ta'adda

'Yan Boko Haram sun kashe sojoji a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan Boko Haram sun kona motocin sojoji

Majiyar ta bayyana cewa marigayi Manjon an tura shi wannan sansani na FOB ne ƙasa da watanni huɗu da suka gabata bayan ya samu ƙarin girma na musamman.

An bayar da rahoton cewa fararen hula uku da ke aikin sake gina ƙauyen sun ji rauni sakamakon harbin da aka riƙa yi, yayin da maharan suka ƙone motocin sojoji da wasu kayan aiki da ke sansanin.

Sojoji sun fafata da 'yan ta'addan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe tsagerun 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram yayin wani kazamin artabu a jihar Borno.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da dakarun Operation Desert Sanity V, tare da hadin gwiwar wasu mambobin CJTF suka kaddamar da farmaki a yankin Shehuri da ke karamar hukumar Konduga.

Dakarun sun gwabza fada da ‘yan ta’addan, inda karfin wutar sojoji ya rinjaye 'yan ta'addan Boko Haram, lamarin da ya kai ga kashe tsageru takwas daga cikinsu, yayin da sauran suka ranta ana kare dauke da raunukan harbin bindiga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng