An So Zuga Malami Ya Fito Takara, Shehi Ya Yi Kaca Kaca da Aka Ce Ya Nemi Gwamna
- Sheikh Abubakar Mukhtar Yola ya nuna rashin jin dadinsa kan kiraye-kirayen da ake yi masa na ya nemi takarar gwamna
- Ya gargadi malamai kan shiga siyasa da cewa yin takara na iya zubar da mutunci da kima a idon mutane da yan siyasa
- Malamin ya jaddada cewa shi kansa bai dace da zama shugaba ba, har ya ce idan aka ji yana neman takara a kai shi asibiti
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa - Wani malamin Musulunci a Adamawa ya yi tsokaci kan kiran neman takarar gwamna da ake yi masa a jihar.
Sheikh Abubakar Mukhtar Yola ya nuna bacin ransa game da kiran da ake yi masa wai ya nemi takara a zaben shekarar 2027.

Source: Facebook
Zancen takara ta fusata Sheikh Abubakar Yola
Legit Hausa ta gano faifan bidiyon malamin ne a shafin Zauren Sheikh Abubakar Muktar Yola da aka wallafa a Facebook.
A bidiyon yayin tafsirin Ramadan, malamin ya nuna bakin cikinsa kan yadda ake zuga malamai su fito takara inda ya ce shi ba kamar wadanda Allah ya jarrabe su da son shugabanci ba ne.
Ya bukaci malamai su ji tsoron Allah saboda shiga siyasa yana zubar masu da mutunci da kima da kuma kauce wa tsarin Annabawa
Ya ce:
"An turo wasiku wai na nemi takarar gwamna, wadanda suke wannan abin su ji tsoron Allah, idan wasu daga cikin malamai Allah ya jarrabe su da son shugabanci, suka ce za su yi ko da mutuncinsu zai zube, za su kauce wa tsarin Annabawa, su je su yi.
"Idan malamai suka ce za su zama shugabanni, su waye za su karantar da al'umma, babu shugaban da ba a zaginsa.
"Ni a ra'ayi na ba na goyon bayan malamai sun shiga takarar gwamna ko shugaban kasa domin abin na cutar da su da kaskantar da su.

Source: Original
'Ban cancanci takara ba' - Sheikh Abubakar Yola
Malamin ya ce ko kadan shi ya san bai cancanci zama shugaba ba inda ya ce akwai yan boko da yawa da suka fi malamai amana.

Kara karanta wannan
Jingir ya yi fito na fito da shirin kafa 'yan sandan jihohi, malamin ya yi zargin munafurci
Ya ce ganin malami yana wa'azi ba shi ne ke nuna yana tsoron Allah ba saboda wasu ba su yi mu'amala da shi suka gani ba.
"Ni na tabbata akwai malamin da idan aka ba shi shugabanci zai cutar fiye da yan bokon, har a masallaci ana korar limamai kan cin amana.
"Don kana ganin malami yana wa'azi, mai tsoron Allah ne, ka zauna da shi ne?, ka yi mu'amala da shi? Ba ka san halayena da laifuffukan da nake yi a boye ba.
"Ni ai yanzu duk ranar da aka ce maka zan nemi gwamna, ku kama ni ku kai ni asibitin mahaukata, saboda ban cancanta ba, idan ka zaben ma sai Allah ya tambaye ka don ba zan iya ba."
- Sheikh Abubakar Mukhtar Yola
Malamin ya ce idan ka fara takara duk abubuwan da ka ce haram ne a baya, haka zaka z kana sauya fatawa domin kawai biyan bukatar kansa ta siyasa.
Pantami ya magantu kan sukar PDP
Mun ba ku labarin cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi magana game da shigar mutanen kirki cikin siyasa tsundum a Najeriya.
Pantami ya bayyana cewa kalubalantar shigarsa siyasa na nuna tasirin da yake da shi, yana cewa tsoron wannan tasiri ne ke sa wasu su nuna adawa.
Tsohon ministan ya kare kansa kan batun Al-Kunut da ya yi a da, yana cewa martaninsa ya samo asali ne daga furucin wani babban jami’in gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

