Albarkar Ramadan: Mercy ta musulunta, ta zama A'isha a garin Yola

Albarkar Ramadan: Mercy ta musulunta, ta zama A'isha a garin Yola

Yayin da musulmai a dukkan fadin duniya ke cigaba da azumtar azumin wata mai falala na Ramadana, tuni dai falalar watan ta fara ratsa zukatan wasu mutanen da da ma musulmai bane suna ta komawa musulmai cikin falalar ubangiji.

Mun samu cewa dai a irin hakan ne ma wata baiwar Allah mai suna Mercy da a da kirista ce ta karbi kalmar shahada sannan kuma ta zabi sunan A'ishatu a garin Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Albarkar Ramadan: Mercy ta musulunta, ta zama A'isha a garin Yola
Albarkar Ramadan: Mercy ta musulunta, ta zama A'isha a garin Yola

KU KARANTA: Naira ta sha kasa a kasuwannin 'yan canji a Najeriya

Legit.ng ta samu cewa ta musulunta ne a wurin tafsirin da Sheikh Abubakar Muktar ke gudanarwa a garin Yola, jihar Adamawa a lokacin da ake kan yin azumi na uku.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Borno dake a yankin Arewa maso gabashin kasar nan Alhaji Kashim Shettima ya sanar da bada umurnin fatattakar dukkan masu ruwa da tsaki da masu shirya cacar nan ta kwallo da wasanni ta NaijaBet a dukkan fadin jihar.

Gwamna Shettima dai ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabin sa a wajen taron karawa juna sani da hukumar gidan radio da talabijin na jihar wato BRTV ta shirya a karo na sha hudu a yau.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng