Kisan Matafiya a Plateau: Gwamna Ya ba da Umarni bayan Tsoron Barkewar Rikici
- Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya umarci hukumomin tsaro su tsananta farautar masu hannu a harin Ratatis da ya kashe aƙalla mutane
- Gwamnan ya ce harin abin takaici ne, yana mai jaddada cewa ya kawo koma baya ga zaman lafiyar da ake samu ta hanyar sulhu
- Bayan harin, fargaba ta mamaye birnin Jos yayin da aka rufe shaguna yayin da jami’an tsaro sun ƙara yawan sintiri
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya nuna damuwa game da harin da aka kai a Plateau wanda ya jawo rasa rayuka.
Gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen aiki tare da kama waɗanda ke da hannu a mummunan harin da aka kai al’ummar Ratatis a Dorowa Babuje, Barkin Ladi, wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum bakwai.

Source: Facebook
Umarnin da Gwamna Caleb ya ba jami'an tsaro
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne cikin wata sanarwa da jaridar Zagazola Makama ta samu wanda kwamishiniyar yada labarai ta Plateau, Joyce Ramnap, ta fitar a Jos.
Mutfwang ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai kiran lamarin da “ta’addanci mara dalili” da kuma koma baya ga zaman lafiyar da aka samu ta hanyar tattaunawa da sulhu.
A cewar sanarwar, gwamnati ta girgiza da samun labarin harin cikin baƙin ciki, inda aka tabbatar da mutuwar fararen hula da ba su ji ba su gani ba a ranar Lahadi, 22 ga Fabrairu 2026.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa waɗanda suka jikkata suna samun kulawa a asibitocin da ke kusa, kuma gwamnati na sa ido kan halin da suke ciki domin tabbatar da ingantacciyar jinya.
Ya kuma ce an kafa rundunar haɗin gwiwa ta bincike da ceto, wacce ta ƙunshi jami’an tsaro da jami’an gwamnati, domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa, gano ɓatattun mutane da kuma daidaita al’ummar da abin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan
Yadda Kashim Shettima ya je Kwara, ya ki ziyartar kauyukan da aka kashe mutane 200

Source: Original
Gwamna Mutfwang ya tura sakon ta'aziyya
Gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, tare da addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata, cewar Punch.
Haka kuma ya umarci hukumomin tsaro da su ƙara tsaro a yankin da abin ya shafa da maƙwabta domin hana sake faruwar rikici.
Ya bukaci mazauna yankin su kasance cikin natsuwa, su kiyaye doka, tare da ba da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin taimaka wa binciken da ake yi.
Sai dai sanarwar ba ta ambaci rahotannin mutuwar wasu Fulani a wasu hare-hare dabam ba, ko kuma kisan wasu mutane huɗu da aka ce an kai musu hari bayan zanga-zangar wasu mazauna yankin.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau
Kun ji cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe Fulani makiyaya tare da sare kan daya daga cikinsu a hanyarsu ta komawa gida.
Kungiyar Miyetti Allah ta yi zargin cewa 'yan kabilar Berom ne suka kai harin, yayin da su kuma matasan Berom suka musanta zargin.
Rundunar soji ta 'Operation Enduring Peace' ta tabbatar da faruwar lamarin sannan ta bayyana matakan da ta dauka zuwa yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
