Jihohin da Suka Rage Lokacin Tashi daga Ofis Alfarmar Watan Ramadan a Najeriya
A ranar 18 ga watan Fabrairu ne aka fara azumin watan Ramadan a Najeriya, wanda ke nufin za a shafe kwanaki 29 ko 30 ana ibada.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Tun bayan da aka fara azumin, wasu daga cikin gwamnonin Najeriya suka dauki matakin rage awannin da ma'aikata ke yi a ofis.
Nigeria - A cikin sanarwar daban-daban da suka fitar, gwamnatocin jihohi sun bayyana cewa an dauki matakin ne domin ba Musulmi damar ibada a cikin nutsuwa.

Source: Facebook
Legit ta tattaro wasu daga cikin gwamnonin kasar nan da suka rage awannin aiki, inda za a fara da:
Jihohin da aka rage lokacin aiki saboda Ramadan
1. Gwamna Abba Kabir Yusuf
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnatin Jihar Kano ta amince da rage awannin aikin ma’aikatan gwamnati domin su samu damar ibada a cikin kwanciyar hankali.
Wannan na kunshe a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 18 ga Fabrairu, 2026, da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jiha ya fitar.

Source: Facebook
Daraktar gudanarwa, Safiyya Suleiman ce ta sanya wa hannu a kan takardar a madadin Shugaban Ma’aikatan gwamnatin jiha.
Takardar, mai lamba HCS/LEV/2/V.II/177 ta bayyana cewa ma’aikatan gwamnati za su riƙa yin aiki da ragin sa’a ɗaya a kowace rana a tsawon watan azumi.
Wannan na nufin daga Litinin zuwa Alhamis, za su rika aiki daga 8.00 na safe zuwa 3.00 na rana, ranakun Juma'a kuma na nan yadda su ke, daga 8.00 na safe zuwa 1.00 na rana.
2. Gwamna Bala Mohammed
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati na tsawon kwanaki 30 na azumi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan tsare-tsare a ofishin Shugaban ma’aikata na jiha, Ismail Ibn L. Garam, ya sanya wa hannu.

Source: Facebook
Sanarwar ta bayyana cewa an dauki matakin ne domin bai wa Musulmi damar kiyaye ka’idojin watan Ramadan tare da kara himma a ayyukan ibada.
3. Gwamna Umar Namadi
Daily Post ta wallafa cewa a jihar Jigawa ma, gwamnatin Malam Umar Namadi ta rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a tsawon watan Ramadan.
Shugaban Ma’aikatan gwamnatin Jiha, Muhammad Dagaceri, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce gwamnan ya amince da rage lokutan aiki domin bai wa ma’aikata karin lokaci su gudanar da ibadarsu yadda ya kamata.
Yanzu ma’aikata za su rika aiki daga karfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana daga Litinin zuwa Alhamis, maimakon karfe 5:00 na yamma kamar yadda aka saba.
4. Gwamna Nasir Idris
Hakazalika, Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan jiha.
Sanarwar ta ce an rage lokutan aiki da awanni biyu a lokacin azumi. Ma’aikata za su rika aiki daga karfe 8:00 na safe zuwa 2:00 na rana daga Litinin zuwa Alhamis.

Source: Facebook
Yayin da a ranar Juma’a za su tashi karfe 12:00 na rana domin ba su damar samun sallar Juma'a da ci gaba da ibada yadda ya kamata.
Shehun Borno ya sanar da fara azumi
A baya, kun samu labarin cewa Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Elkanemi ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya ranar Talata, 17 ga Fabrairun 2026.
Sai dai hakan wani sabon abu ne da ba a saba gani ba domin an saba jin sanarwa ne kai tsaye daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III a garin Sokoto.
Tuni dai mafi yawan musulmi a Najeriya suka tashi da azumi a ranar Laraba, 1 ga watan Ramadan, 1447AH daidai da 18 ga watan Fabrairu kamar yadda aka sanar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


