Ramadan: Coci Ya Yi Abin Alheri, Ya Raba wa Musulmi, Makarantun Tsangaya Kayan Abinci
- Wani cocin Kirista ya yi abin alheri ga al'ummar Musulmi yayin da fara azumin watan Ramadan a jihar Kaduna
- Cocin ya rabawa Musulmai sama da 1,000 kayan abinci gabanin Ramadan 2026 domin tallafa wa marasa galihu
- Fasto Yohanna Buru ya ce shirin na daga cikin kokarin inganta zaman lafiya da hadin kai tsakanin addinai a Arewacin Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna – Wani cocin Kirista da ke Kaduna ya farantawa wasu daga cikin al'ummar Musulmi yayin da aka fara azumin Ramadan.
Cocin ya raba wa Musulmai tallafi yayin da aka fara azumin Ramadan na shekarar 2026 a yau Laraba 18 ga watan Fabrairun 2026.

Source: Original
Fasto ya raba kayan abinci ga Musulmi
Rahoton Legit.ng ya ce cocin ya yi haka ne domin karfafa zaman lafiya da fahimtar juna yayin ibadan azumi.
An gudanar da rabon kayan abincin ne a Masallacin hanyar Kano da ke Kaduna, inda aka bai wa Musulmai, makarantun Tsangaya da wasu ‘yan gudun hijira tallafi.
Cocin 'Church of Christ Evangelical and Life Intervention Ministry' da ke Sabon Tasha ta jagoranci shirin, inda ya raba hatsi da sauran kayan masarufi.
Babban Faston cocin, Dakta Yohanna Buru, ya ce suna yin hakan ne duk manyan lokutan gabatar da wani bikin addinai domin tallafa wa mabukata.
Ya bayyana cewa sun shafe kusan shekaru ashirin suna irin wannan taimako a Arewacin Najeriya, musamman a watan Ramadan.
A cewarsa, baya ga kayan abinci, suna kuma bayar da darduma da bokiti tare da bukatar a yi addu’ar zaman lafiya.
Ya ce sun hada kai da limamai da fastoci domin wayar da kan ‘yan kasuwa su sassauta farashi a kasuwanni.

Source: Original
Yadda Fasto ke taimaka wa Musulmi
Hakazalika, ya ce a wasu shekarun sun taimaka wa fursunoni Musulmai domin su samu damar haduwa da iyalansu a Ramadan.
Ya kuma yaba wa wata baiwar Allah, Hajiya Ramatu Tijjani, bisa taimakon da take ba zawarawa da marayu a lokacin Kirsimeti.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun bayyana godiya, suna cewa taimakon ya zo a kan lokaci mai muhimmanci.
Malam Hassan Lawal, jagoran masu nakasa a Kaduna, ya ce tallafin yana taimakawa wajen saukaka musu ibada cikin kwanciyar hankali.
Shi ma Malam Tukur Zubairu daga bangaren makafi ya yaba da yadda cocin ke ci gaba da tallafa musu tsawon shekaru.
Imam Ibrahim Musa wanda ya wakilci makarantun Tsangaya ya gode tare da kira ga sauran jama’a su koyi darasi daga wannan misali.
Wannan ba shi ne karon farko ba da Faston ke rabon kayan abinci ga al'ummar Musulmi a watan Ramadan, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Kiristoci sun ba Musulmi abincin buda baki
Mun ba ku labarin cewa wasu gungun matasa Kiristoci sun raba abinci ga al’ummar Musulmi a lokacin da suke buda bakin azumin watan Ramadan a Senegal.
Wadanda ake ba abincin galibi mutane ne da ke kan hanyar wucewa yayin da aka ga matasan na raba abincin ga masu ababen hawa da fasinjoji.
Hakan ya taimaka musu wajen buda baki yadda ya kamata domin ba za su samu damar isa gidajensu ba kafin lokacin buda bakin.
Asali: Legit.ng

