A zauna lafiya: Bidiyon Kiristoci na raba wa Musulmi abincin buda baki ya girgiza intanet

A zauna lafiya: Bidiyon Kiristoci na raba wa Musulmi abincin buda baki ya girgiza intanet

  • An ga wasu gungun matasa kiristoci suna raba abinci ga al’ummar musulmi a lokacin da suke buda bakin azumin watan Ramadan a kasar Senegal
  • Wadanda ake ba abincin galibi mutane ne da ke kan hanyar wucewa yayin da aka ga matasan na raba abincin ga masu ababen hawa da fasinjoji
  • Hakan zai taimaka musu wajen buda baki yadda ya kamata domin ba za su samu damar isa gidajensu ba kafin lokacin buda bakin

Tawagar matasa kiristoci sun hada kansu don su yi abin da mutane da yawa suka kwatanta da halin kirki.

Sun raba abinci ga al’ummar musulmi da ke kan hanyar wucewa domin samun damar yin buda baki na azumin watan Ramadan. Abin sha'awa kamar wannan dai ya faru ne a Dakar, Senegal.

Zaman lafiya tsakanin musulmi da kirista
A zauna lafiya: Bidiyon Kiristoci na raba wa Musulmi abincin buda baki ya girgiza intanet | Hoto: @trtworld
Asali: Instagram

Kirista da Musulmi na da kyakkyawar alaka

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Ja Hankali

Wani faifan bidiyo da aka gani a yanar gizo ya nuna yadda matasan ke rabawa masu ababen hawa da fasinjoji fakitin kayan ciye-ciye, suna sanya murmushi a fuskokinsu.

Musulmi da Kirista a Senegal an ce na da kyakkyawar alaka. Iyalai da yawa an ce akan samu surkin Musulmi da Kirista a cikinsu.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan soshiyal midiya

Jama'a a intanet sun mayar da martani kan bidiyon da @trtworld ya yada, inda suka shiga sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu.

Karanta kadan daga cikin martanin jama'a a kasa:

@in.the.shadows.of.malec ya ce:

"Abin ban mamaki ne ganin haka."

@generouspappi yayi sharhi da cewa:

"A zahiri za mu iya kirkirar duniya mai cike da zaman lafiya ga karan kawunanmu."

@nourom.ar ya mayar da martani da cewa:

Kara karanta wannan

Inda ranka: Tashin hankali yayin da wani ya bude asusunsa ya ga takardu a madadin kudi

"Jinjina. Mu duka mutane ne kuma ya kamata mu kula da kasarmu ba tare da duba addini ba .. a duk inda muke a duniya."

@x.a_ray_of_light.x ya ce:

"Haka ya kamata... Girmama juna da taimakon juna... Wannan shi ne abin da Musulunci da sauran littattafan Allah na gaskiya suka koya mana... Wannan shi ne dan Adamtaka."

@kahfy_ateecck ya ce:

" A yada soyayya da kaunar juna. Abin ban mamaki."

@sureyyadalgin ya ce:

"Kuma shin matasan musulmi suna aikata irin wannan abu ga sauran addinai? in haka ne ajinjina gare su duka."

Diyar tsohon Sarkin Kano Sanusi II da ke Saudi ta bayyana wani mummunan halin Larabawa

A wani labarin, daya daga cikin ‘ya ‘yan Mai martaba Muhammadu Sanusi II, Shahida Sanusi ta zargi Larabawa da nuna bambanci da wariyar launin fata.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Shahida Sanusi mai zama a Saudi Arabia ta na zargin mutanen kasar Larabawa da nunawa sauran jama’a bambanci.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya

Hajiya Shahida Sanusi ta jefi Larabawa da wannan zargi ne yayin da ta ke amsa tambayoyin mutane a kan shafinta na sada zumunta na Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel