Wata Sabuwa: Minista Ya Fatattaki Wasu Daraktoci a Ma'aikatar Gwamnatin Tarayya
- Gwamnatin tarayya ta bada umarnin sallamar dukkan daraktocin ma'aikatar lafiya da suka shafe shekaru takwas akan kujerunsu
- Dole ne daraktocin da abin ya shafa su mika kayan gwamnati da ke hannunsu, su kuma maida albashin da aka biya su kwanan nan
- Sabuwar dokar ma'aikatan gwamnatin tarayya ta shekarar 2021 ta kayyade wa'adin aiki ga manyan sakatarori da kuma daraktoci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ministan lafiya, Muhammad Ali Pate, ya bada umarnin sallamar dukkan daraktocin ma'aikatar lafiya ta tarayya da suka shafe aƙalla shekaru takwas a wannan matsayi.
Waɗanda wannan umarni ya shafa sun haɗa da daraktoci a ma’aikatar kanta, asibitocin tarayya, da kuma hukumomin dake ƙarƙashin ma'aikatar.

Source: Facebook
An fatattaki daraktoci a ma'aikatar tarayya
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar daga ofishin babban sakataren ma'aikatar, Tetshoma Dafeta, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
A ranar Litinin ne aka bada rahoton cewa gwamnatun tarayya ta umarci dukkan ma’aikatu, rassa, da hukumomi (MDAs) da su aiwatar da dokar shekaru takwas na wa'adin daraktoci da manyan sakatarori.
Sanarwar Tetshoma Dafeta ta ce:
“Wannan umarni ya shafi dokar wa’adin shekaru takwas ta ma’aikatan gwamnatin tarayya, wacce ta wajabta ritayar dole ga daraktoci bayan shekaru takwas a wannan matsayi.
“Dole ne dukkan jami’an da abin ya shafa wadanda suka kammala shekaru takwas a matsayin daraktoci tun daga ranar 31 ga watan Disamba, 2025, su bar aiki nan take.”
A cikin sanarwar, an buƙaci dukkan shugabannin hukumomi su tabbatar da cewa ma’aikatan da abin ya shafa sun miƙa dukkan takardun hukuma da kayan gwamnati dake hannunsu ba tare da ɓata lokaci ba.
Matakan hana albashi da mayar da kuɗi
Haka zalika, an ba da umarnin dakatar da albashin daraktocin ta hanyar tsarin IPPIS, sannan aka wajabta musu mayar wa baitul-mali dukkan alawus-alawus ɗin da aka biya su bayan ranar da ya kamata su bar aiki.
Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da ofishin shugabar ma’aikatan tarayya ya bayar ranar 10 ga watan Fabrairu, 2026, domin zama jagora ga dukkan hukumomi.
Bugu da ƙari, an buƙaci hukumomin da su aika da sunayen dukkan jami'a da ke a matakin darakta (CONMESS 07/CONHESS 15/CONRAISS 15) zuwa adireshin imel na ma'aikatar don gudanar da bincike.
“Duk wanda ya gaza bin umarnin da aka bayar a sakin layi na biyu (wanda ya bada umarnin barin aiki nan take), zai fuskanci tsauraran takunkumi daga hukumomin da abin ya shafa.”
- Tetshoma Dafeta.

Source: Twitter
Tarihin sabuwar dokar PSR
A watan Yulin 2023, tsohuwar Shugabar Ma’aikata ta Tarayya, Folasade Yemi-Esan, ta sanar da fara aiki da fasalin dokokin ma’aikatan gwamnati (PSR) wanda aka yi wa kwaskwarima, in ji rahoton The Sun.
Yemi-Esan ta bayyana cewa sabuwar dokar ta fara aiki ne tun daga ranar 27 ga Yulin 2023, bayan amincewar da Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta yi tun a shekarar 2021.
A ƙarƙashin sashe na 020909 na sabuwar dokar, wa'adin manyan sakatarori ya koma shekaru huɗu, tare da yiwuwar sabuntawa sau ɗaya kawai idan mutum ya yi aiki mai gamsarwa.
Haka zalika, dokokin sun tanadi cewa darakta (matakin GL 17) ko makamancin sa dole ne ya yi ritaya idan ya shafe shekaru takwas a kan wannan kujerar.

Kara karanta wannan
"Ƙila don ya ƙi APC ne": El Rufa'i ya yi tir da kai sunan Kwankwaso majalisar Amurka
Minista ya nuna sha'awar takarar gwamna
A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2027.
A wata hira da ya yi da manema labarai, Ali Pate ya bayyana cewa zai iya fitowa takara idan masu ruwa da tsaki a siyasar Bauchi suka goyi bayansa.
Duk da wannan kuduri, Ali Pate ya ce a halin yanzu ya mayar da hankali kan aikin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba shi na jagorantar ma’aikatar lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

