‘Yana Bukatar Rukiyya’: Sanata Kawu Sumaila Ya Faɗi Halin da Ado Doguwa ke Ciki

‘Yana Bukatar Rukiyya’: Sanata Kawu Sumaila Ya Faɗi Halin da Ado Doguwa ke Ciki

  • Abdulrahman Kawu Sumaila ya roki jama’a su guji mayar wa Alhassan Ado Doguwa martani, yana cewa yana fuskantar wata matsala
  • Sanatan ya ce wasu abubuwa da suka faru a baya ne suka taru a kansa, yana mai jaddada cewa na kusa da shi sun dade da lura da halayensa
  • Kawu ya kuma gargadi magoya baya su daina tsokanar Doguwa, yana mai cewa abin da yake bukata yanzu shi ne goyon baya da addu’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila daga jihar Kano ya yi magana game da halin da Hon. Alhassan Ado Doguwa ke ciki.

Kawu Sumaila ya yi martanin ne bayan mutane suna ta kiransa kan Doguwa saboda maganganu da ya yi a taron APC ko bayan haka a Kano.

Kara karanta wannan

NiMet ta gargadi kamfanonin jiragen sama, ta hango matsala a Kano da jihohi 10

Kawu Sumaila ya fadi halin da Ado Doguwa ke ciki
Sanata Kawu Sumaila daga jihar Kano. Hoto: Senator Kawu Sumaila Reporters.
Source: Twitter

Sanatan ya bayyana haka ne a wani bidiyo da tashar Premier Radio ta wallafa a shafin Facebook a jiya Litinin 16 ga watan Faburairun 2026.

Kawu Sumaila ya fadi halin da Doguwa ke ciki

A cikin bidiyon, Kawu Sumaila ya bukaci magoya bayansu da sauran al'mma su yi hankali da Hon. Ado saboda matsalar da yake ciki.

Ya ce:

"Watakila abubuwan da aka tattauna ne a taron da muka yi bai masa dadi ba, ni wannan abu bai zo min da mamaki ba, domin na kusa da shi da abonmu muna tattauna wannan hali da yake ciki.
"Wannan ya sake tabbatar da abin da muke zargi kansa, Alhassan yana da matsaloli kwarara cuta guda biyu, dole ne mu tsaya mu yi addu'a Allah ya yi masa maganinsu.
"Daya tana da wuyar warkewa, daya kuma addu'a da neman magani zai iya warkar da ita, ina kira da abokanmu, yan uwa da abokan arziki mu matsa da yi wa Alhassan rukiya."

Kara karanta wannan

Shirin da ya kamata Musulmai su yi kafin 1 ga watan Ramadan

Kawu Sumaila ya bukaci addu'o'i ga Alhassan Ado Doguwa
Sanata Kawu Sumaila da Hon. Alhassan Ado Doguwa. Hoto: Hon. Alhassan Ado Doguwa, Senator Kawu Sumaila Reporters.
Source: Facebook

Doguwa: Shawarar Kawu Sumaila ga abokansa

Sanatan ya yi kira da abokansu da ka da kowa ya rika yi wa Alhassan Ado martani inda ya bukaci kara yin hakuri da abubuwan da yake yi.

Ya ce abubuwan na kara yawan wanda ka iya sanya wa ya fara kai duka saboda akwai wasu kalamai da su kadai yake son ji a rika fada masa.

"Ina ganin abubuwan da suka faru a baya su ke taruwa a kan Alhassan har ya zo yana irin wadannan abubuwa.
"Ina kira ka da wani daga cikin masoyanmu martani, a yi masa hakuri, a yi masa uzuri, ina son duk masu mu'amala da shi su yi hakuri da shi kaddara ce kowa zai iya fadawa ciki.
"Ina son a taya shi da addu'a Allah ya farkar da shi ya daina irin wannan abubuwa da yake yi, sannan mutane su bar kokarin tsokanar Ado ka da ya fara duka."

Kara karanta wannan

Trump ya taso Ali Khamenei a gaba, ya tabo batun tuge shi a jagorancin Iran

- Kawu Sumaila

Sanata Sumaila ya ce Alhassan ba zai fahimci yana cikin wani hali ba saboda haka lalurar take, inda ya ce addu'a da hakuri yake bukata.

Ya ce maganar da yake son ji a kullum shi ne 'sai ka yi dan Ado' yana son irin wannan maganar saboda son tabbata a kan kujerar majalisa.

Kawu Sumaila ya musanta zargin butulce wa NNPP

An ji cewa Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila ya bayyana cewa ficewarsa daga jam’iyyar NNPP na da alaka ta kai tsaye da mutanen Kano ta Kudu.

A cewarsa, ya yanke shawarar barin jam’iyyar ne saboda yana son ci gaba da kawo wa mazabarsa mafita da ci gaba da ba zai samu a NNPP ba.

Ya ce ko da yake ya fice daga jam’iyyar da ke mulki a Kano, hakan ba zai kawo wata matsala a dangantakarsa da gwamnatin jihar ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.