Jerin Shugabannin da Suka Rike Hukumar NAHCON da dalilin Saukarsu daga Kujerar

Jerin Shugabannin da Suka Rike Hukumar NAHCON da dalilin Saukarsu daga Kujerar

An kafa hukumar alhazai ta Najeriya, NAHCON a 2006 wanda ta samu shugabanni guda shida ciki har da sabon shugabanta Ambasada Isma'ila Abba Yusuf.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An kafa hukumar alhazai ta NAHCON a shekarar 2006 domin kula da jigilar Musulmi zuwa kasa mai tsarki saboda aikin hajji.

Tun daga wancan lokaci, akalla shugabanni guda shida ne suka jagoranci hukumar ciki har da wanda aka nada sabo a yanzu, Ambasada Isma'ila Abba Yusuf.

Jerin shugabannin addini da suka rike kujerar NAHCON
Sabon shugaban NAHCON, Isma'ila Abba Yusuf, Mohammed Musa Bello da Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan. Hoto: FCTA, National Hajj Commission of Nigeria.
Source: Facebook

Rahoton Leadership ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada Isma'il Abba Yusuf a matsayin sabon shugaban hukumar.

Hakan ya biyo bayan murabus din Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan daga kujerar bayan zargin badakala a karkashin jagorancinsa.

Tun bayan hawan shugaba Bola Tinubu kan karagar mulki, ya nada shugabannin hukumar alhazai har guda uku.

Kara karanta wannan

'Mulki mafi muni,' Hakeem Baba Ahmed ya yi gargadi kan tazarcen Tinubu a 2027

Shugabannin da suke rike kujerar NAHCON

Legit Hausa ta duba shugabannin da suka rike hukumar da ake yawan samun matsaloli da kuma dalilin barin su kujerar.

1. Mohammed Musa Bello

Tsohon ministan birnin tarayyar Najeriya, Abuja shi ne ya fara rike shugabancin hukumar alhazai bayan kafa ta a 2006.

Mohammed Musa Bello ya fara rike shugabancin hukumar daga shekarar 2006 har zuwa 2015 kafin sauka daga kujerar.

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ne ya nada Mohammed Musa Bello wanda ya rike mukamin har 2015, cewar Daily Trust.

Ya bar kujerar bayan marigayi Muhammadu Buhari ya saka sunansa cikin jerin ministoci wanda ya rike mukamin ministan Abuja daga 2015 zuwa 2023.

Tsohon minista da ya fara rike mukamin hukumar NAHCON
Tsohon ministan Abuja, Mohammed Musa Bello. Hoto: @MuhdMusaBello.
Source: Twitter

2. Abdullahi Mukhtar Muhammad

Abdullahi Mukhtar Muhammad shi ne shugaban hukumar na biyu bayan Mohammed Musa Bello ya zama minista a Najeriya.

Abdullahi Mukhtar ya rike shugabancin hukumar ne na tsawon shekaru hudu kacal kafin Muhammadu Buhari ya nada wani shugaban.

Kara karanta wannan

Bayan taawon kwanaki, an ji dalilin kwace fasfon Malam El Rufai a filin jirgin Sama

An ce tsohon shugaban hukumar alhazai a Kaduna ya yi kokari sosai wurin dakile wasu badakaloli da matsaloli a cikin hukumar.

Sai dai shi ma ya fuskanci kalubale saboda a majalisar tarayya ta kafa kwamiti domin bincikensa kan zargin badakala a aikin hajjin 2016.

Daily Post ta ce Abdullahi Mukhtar ya bar kujerarsa ne bayan karewar wa'adinsa wanda aka maka gwamnatin tarayya, NAHCON a kotu kan zargin kara masa wa'adin wata shida ba bisa ka'ida ba.

Yadda tsofaffin shugabannin NAHCON a Najeriya suka kawo sauye-sauye
Tsohon shugaban NAHCON na 2 a Najeriya bayan kafa ta, Abdullahi Mukhtar Muhammad. Hoto: National Hajj Commission of Nigeria.
Source: Facebook

3. Zikrullah Kunle Hassan

An nada tsohon Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Osun a matsayin shugaban hukumar a shekarar 2019, Muslim News ta ruwaito.

Ya yi aiki na tsawon shekaru huɗu kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo sauyi a Hukumar NAHCON, lamarin da ya sake fasalta tsarin jagorancin hukumar.

Bayan barinsa aiki a watan Janairun 2024, tambayoyi sun ci gaba da tasowa kan yadda ya bar muƙamin.

Wasu rahotanni sun zarge shi da cewa Hukumar EFCC ta gayyace shi kan zargin almundahana a wancan lokaci.

Kara karanta wannan

Shettima ya fadi sakon Tinubu da manyan jiga jigai suka tarbi Gwamna Abba zuwa APC a Kano

Sai dai Hassan ya sha musanta aikata wani laifi, yana mai cewa jami’an EFCC sun duba takardun kuɗaɗen hukumar ne kawai tun yana kan kujerarsa.

Zikrullah na daga cikin wadanda suka kawo sauyi a NAHCON
Tsohon shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Kunle Hassan. Hoto: National Hajj Commission of Nigeria.
Source: Facebook

4. Jalal Ahmad Arabi

Jalal Arabi shi ne tsohon hadimin ga Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Mataimakin Darakta a Ma’aikatar Tsaro da kuma babban sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa kafin zama shugaban NAHCON.

Jalal Arabi, ya kama aiki a matsayin shugaba a shekarar 2023, a lokacin da hukumar ke fama da ƙalubalen cikin gida bayan cire wanda ya gabace shi.

Sai dai cikin shekara guda, NAHCON ta sake tsunduma cikin sababbin ce-ce-ku-ce da suka sake jefa shugabancinta cikin tambayoyi.

Lamarin ya kai ga wasu gwamnoni suka jagoranci sukar hukumar kan zargin rashin kyakkyawan tsari da gudanarwa.

Yadda zargin badakala ta raba Arabi da kujerarsa a NAHCON
Tsohon shugaban NAHCON a Najeriya, Jalal Ahmad Arabi. Hoto: National Hajj Commission of Nigeria.
Source: Twitter

5. Farfesa Abdullahi Usman Pakistan

Sheikh Abdullahi Usman Pakistan ya hau kujerar shugabancin NAHCON a shekarar 2024, a lokacin da hukumar ke fuskantar manyan matsalolin gudanarwa da rashin tsari.

Daga cikin matsalolin da suka addabi hukumar akwai ƙarancin abinci, ƙarin kuɗin tafiye-tafiye, rage kuɗin BTA da aka yi wa alhazai alkawari, da kuma zargin rashin kyakkyawan tafiyar da kuɗi da cin hanci.

Kara karanta wannan

Aminu Vs Sanusi II: Gwamna Abba ya sake tabo batun rikicin sarautar Kano a gaban Sanata Barau

Farfesa Usman ya fuskanci turjiya daga cikin gida fiye da wasu shugabannin da suka gabace shi, cewar The Guardian.

Abokan hamayyarsa sun zarge shi da rashin bin ka’idojin sarrafa kuɗi, rashin bayyana gaskiya da kuma karya dokokin kula da kuɗaɗen jama’a wanda daga baya ya yi murabus.

Dalilin da Sheikh Pakistan ya yi murabus a shugabancin NAHCON
Tsohon shugaban NAHCON da ya yi murabus, Sheikh Abdullahi Saleh Usman Pakistan. Hoto: National Hajj Commission of Nigeria.
Source: Facebook

6. Ambasada Isma'ila Abba Yusuf

Isma'ila Abba Yusuf shi ne shugaba na shida da aka nada a hukumar tun bayan kirkirarta a shekarar 2006 watau mulkin Olusegun Obasanjo.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Ismaila Abba Yusuf a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa a yau Laraba, 11 ga Fabrairun 2026.

Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ya nuna cewa sabon shugaban zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Saleh Usman da ya jagoranci hukumar a baya.

Mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana cewa Bola Tinubu ya tura takarda ga majalisar dattawa domin tantance sabon shugaban da ya nada.

Kara karanta wannan

Atiku ya lura da kuskuren INEC, ya bukaci a sauya lokacin zaben 2027

Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar NAHCON
Sabon shugaban hukumar NAHCON, Ismaila Abba Yusuf. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

NAHCON: An hango matsala bayan saukar Sheikh Pakistan

A wani labarin, masu gudanar da aikin Hajji sun nuna damuwa kan sauyin shugabanci a hukumar NAHCON gab da fara aikin Hajjin shekarar 2026 da muke ciki.

Sun ce murabus din shugaban NAHCON na iya kawo cikas ga shirye-shiryen da aka kusa kammalawa wanda na daf da zuwa karshe.

Kungiyar ta roki Gwamnatin Tarayya ta bari a kammala shirye-shiryen domin gudun tangarda a aikin Hajjin bana ta 1447.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.