‘Ko Kofa Babu Gidansa na Kano’: Obasanjo game da Zuhudun Marigayi Murtala Mohammed

‘Ko Kofa Babu Gidansa na Kano’: Obasanjo game da Zuhudun Marigayi Murtala Mohammed

  • Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce kisan Janar Murtala Mohammed ya fallasa gazawar tsaro a Najeriya
  • Obasanjo ya bayyana cewa wasu daga cikin masu juyin mulkin na 1976 makusanta ne ga Murtala Mohammed
  • Ya jaddada cewa ci gaban Afirka na bukatar shugabanci nagari da karfafa al’umma, yana mai cewa Afirka ta balaga amma har yanzu tana kan tafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana kyawawan halayen marigayi Murtala Mohammed kafin rasuwarsa.

Obasanjo ya ce kisan gillar da aka yi wa Murtala Ramat Mohammed ya fallasa gibi a tsarin tsaron ƙasa, wanda ya sa aka sake tsara gine-ginen tsaron Najeriya baki ɗaya.

Obasanjo ya yaba halayen Murtala Mohammed
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo. Hoto: @obi_Nwosu.
Source: Facebook

Obasanjo ya tuna kisan Murtala Mohammed

Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abuja yayin Laccar Tunawa da marigayin da taron shugabanci mai taken “Shin Afirka Ta Balaga?”, wanda gidauniyar Murtala Mohammed ta shirya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

IFAD: Ministan Tinubu ya samu gagarumar nasara, an ba shi babban mukami a duniya

Ya tuna da juyin mulkin Fabrairun 1976, yana mai cewa kisan Murtala ya girgiza shugabanci tare da tilasta musu su fuskanci gaskiyar sakaci a bangaren tsaro.

A cewarsa:

“Lokacin da aka kashe Murtala, ina nan. Babu abin da ya rage mini a gwamnatin soja. Mun yi iya bakin kokarinmu.”

Ya kara da cewa dole suka waiwayi baya domin gano inda suka yi kuskure, inda suka fahimci akwai sakaci mai tsanani a tsaro, wanda ya tsara matakan da suka dauka daga baya.

Obasanjo ya fadi yadda marigayi Murtala ya ki karbar kyautar gida
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da marigayi Murtala Mohammed. Hoto: Universal History Archive, PIUS UTOMI EKPEI.
Source: UGC

'Kyawawan halayen marigayi Murtala Mohammed'

Obasanjo ya ce wasu daga cikin masu shirya juyin mulkin sun kasance makusantan marigayi tsohon shugaban ƙasa, ciki har da hadiminsa da abokin karatu a Kwalejin Tsaro.

Ya bayyana cewa lamarin ya nuna muhimmancin sanya kariyar hukumomi sama da dogaro da amincewa kai tsaye tsakanin mutane, cewar The Nation.

Game da yakin basasa, Obasanjo ya ce rikice-rikicen cikin gida a gwamnatin tarayya sun kusa kassara kokarin yaki, yana mai cewa sai da suka ce, “Mu fara gyara gidanmu.”

Ya yabawa Murtala Mohammed da abokan aikinsa, yana mai cewa sun kasance masu kishin kasa da bin doka, tare da rayuwa mai sauki.

Kara karanta wannan

Sanata ya shawarci Musulmi kan yadda za su kalubalanci malamai

A cewarsa:

“Gidan Murtala a Kano ba shi da kofa, kuma ya ki karbar gidan baki na gwamnati saboda ya ga ya cika da kayan alatu.”

Obasanjo ya ce babbar nasarar Murtala ita ce barin wanda zai ci gaba da tafiyarsa, yana mai cewa shugabanni bayan sa ciki har da shi kansa sun gaza yin hakan.

Kan batun ci gaban Afirka, ya ce sauya manufofi akai-akai ya hana nahiyar ci gaba, yana misalta dage haramcin shigo da shinkafa bayan 1979.

IBB ya magantu kan kisan Murtala Mohammed

A baya, kun ji cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana wasu muhimman batutuwa a kan kisan tsohon shugaban kasa, Janar Muhammad Ramat.

An kashe tsohon shugaban ne a ranar Juma'a, 13 ga watan Fabarairu na shekarar 1976, inda aka yi wa motar da yake ciki ruwan alburusai.

Janar IBB mai ritaya ya tabbatar da cewa an fara shirin kashe shugaban ne tun daga lokacin da ya karɓi mulkin kasa a shekarar 1975.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.