Ministan Tinubu Ya Tada Jijiyoyin Wuya, An Yi Rigima da Shi a Zaman 'Yan Majalisa
- Ministan Ayyuka, David Umahi ya halarci zaman kwamitin Majalisar dattawa domin kare kasafin kudin 2026 na ma'aikatarsa
- Yayin zaman kare kasafin, Ministan ya yi musayar yawu da Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole har sai da aka shiga tsakani
- Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi, ya zauna a Majalisar dattawa na tsawon watanni biyu kafin daga bisani ya karbi mukamin minista
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - An samu ɗan rikici a Majalisar Dattawa a ranar Laraba yayin da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, da Sanata Adams Oshiomhole suka yi musayar kalamai masu zafi a lokacin zaman kare kasafin kuɗi.
Lamarin ya faru ne yayin da ministan ke amsa tambayoyin ‘yan majalisa kan kuɗaɗen ayyukan tituna da hanyoyin da suka hada bangarori da dama a faɗin ƙasar.

Source: Facebook
Abin da ya jawo rikici da minista a Majalisa
Leadership ta rahoto cewa rikicin ya fara ne lokacin da Oshiomhole ya tabo batun hanyoyin samar da kuɗaɗe, inda Umahi ya ce ma'aikatarsa ba ta samun kasafin da ya kamata.
Oshiomhole ya ce:
“Ka ce Ministan Kuɗi, wanda Shugaban Ƙasa ya ɗora wa alhakin daidaita tattalin arziki, ba ya sakin kuɗi, kuma hakan na shafar ayyukanka. Amma ka tabbatar mana cewa shugaban kasa bai san da wannan ba, haka ne ka faɗa a jawabin ka na farko.”
Da yake martani, Umahi ya tambayi Oshiomhole, "Yallabai, kana yanke hukunci ne ko kuma tambaya kake yi mini?”
Nan take Oshiomhole ya mayar da martani da cewa: “Ba ka da ikon katse ni.”
Umahi da Oshiomhole sun yi musayar yawu
Takaddamar ta ƙara tsananta lokacin da Umahi ya nuna rashin jin daɗi kan kalaman Sanata Oshiomhole, wanda ya ce ba su dace ba, kamar yadda tashar Arise TV ta kawo labarin.
“A’a, ba za ka yi mini magana da kalamai marasa kyau ba. Ba za ka yi mini magana ta wannan hanya ba, ina da mutunci a Najeriya.” in ji Umahi.
Mataimakin Shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa, Sanata Rufai Hanga (NNPP, Kano ta Tsakiya), ya shiga tsakani tare za gargaɗin ministan.
“Ka kula da kalamanka, don Allah. Kana magana da sanata ne, ka kiyaye kalamanka, ka taɓa zama a wannan Majalisar, don haka ka san me zai rika fitowa daga bakinka. Ka zauna tsawon watani biyu a majalisar nan kafin ka tashi,” in ji Hanga.
Takaddamar ta ɗan dakatar da zaman na ɗan lokaci kafin daga bisani aka dawo da zaman cikin natsuwa, aka ci gaba da kare kasafin kuɗin.

Source: Twitter
Sanata Natasha ta dauki zafi a zaman kwamiti
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi cacar baki mai zafi da shugaban kwamitin kula da harkokin ma'adanai a zaman kare kasafin kudi.
Lamarin ya faru ne bayan shafe kusan sa’o’i huɗu ana tattaunawa a zaman da kwamitin ya shirya domin kare kasafin kudi Ma’aikatar Raya Masana’antar Ƙarafa.
Rahoto ya nuna cewa Natasha ta nuna fushin ta ne lokacin da shugaban kwamitin, Sanata Patrick Ndubueze ya nemi dakatar da ita saboda ta dauki tsawon lokaci tana tambayoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

