Wata Sabuwa: Ministan Tinubu Ya Sha Alwashin Yin Murabus daga Mukaminsa, an Ji Dalili

Wata Sabuwa: Ministan Tinubu Ya Sha Alwashin Yin Murabus daga Mukaminsa, an Ji Dalili

  • An titsiye Ministan ayyuka, David Umahi, da tambayoyi yayin da yake kare kasafin kudin ma'aikatarsa a gaban kwamitin majalisar tarayya
  • 'Yan majalisa sun so jin ba'asi kan yadda aka sauya dan kwangilar da ke aikin wani bangare na titin Abuja zuwa Kaduna
  • Yayin da ba da amsar tambayoyi, David Umahi, ya sha alwashin ajiye aikinsa idan aka samu matsala a aikin

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan ayyuka a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, David Umahi, ya sha alwashin yin murabus daga mukaminsa.

David Umahi ya sha alwashin cewa zai yi murabus daga mukaminsa idan har aka samu cewa aikin hanyar Abuja–Kaduna–Kano da ake gudanarwa bai inganta ba.

Umahi ya sha alwashin yin murabus kan aikin titin Abuja zuwa Kano
Ministan ayyuka na tarayyar Najeriya, David Umahi Hoto: Engr. David Nweze Umahi
Source: Twitter

Umahi ya bayyana hakan ne yayin da yake kare kasafin kudin ma'aikatarsa a gaban kwamitin hadin gwiwa na mambobin majalisar tarayya a ranar Laraba, 11 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun riƙewa minista wuta a kan 'bacewar' kayan Gwamnatin Tarayya

David Umahi ya bayyana cewa a shirye yame ya bari masu gwaji su gudanar da bincike kan ingancin aikin da ake yi.

An titsiye Minista da tambayoyi a majalisa

Yayin zaman, an yi tambayoyi game da bayar da wani bangare na aikin ga wani kamfani da wasu ’yan majalisa suka siffanta da cewa ba a san shi ba, sannan a baya ya shahara ne wajen sayar da injinan samar da wutar lantarki (janareto).

Sanata Adams Oshiomhole (APC/Edo ta Arewa) ya bukaci sanin dalilin da ya sa aka karbe kwangilar daga hannun sanannen kamfanin gine-gine aka ba wa wani kamfani wanda ba a san shi ba.

Tsohon gwamnan na jihar Edo ya kafa hujjar cewa kamfanin bai yi suna ba a harkar gina hanyoyi, jaridar The Sun ta kawo labarin.

David Umahi ya kare kansa

Da yake mayar da martani, Umahi ya yi watsi da damuwar da aka nuna kan asalin dan kwangilar, inda ya jaddada cewa ya kamata a mayar da hankali kan ingancin aikin da aka yi maimakon ra'ayin mutane.

Kara karanta wannan

Dan bindiga da ya kashe Musulmi 51 a masallaci ya fadi dalilin amsa laifinsa

“Yanzu ne ma nake jin sunan Maikano a karon farko. Ko akuyoyi suke sayarwa ko shanu, suna gudanar da aiki da kyau."
"Na gamsu da ingancin aikin da ake yi a bangaren Abuja zuwa Kaduna, kuma ina kalubalantar ku da mu je mu duba. Ku zo da kwararrunku masu binciken ingancin kankare. Idan kuka gwada aka samu matsala, zan ajiye aikina."

- David Umahi

Umahi ya yi bayani

Umahi ya bayyana cewa babban abin lura ba shi ne ko an yi amfani da kankare ko kwalta ba, a’a, batun shi ne shin an sanya ido yadda ya kamata domin tabbatar da karkon aikin.

David Umahi ya sha alwashin hakura da mukaminsa
Ministan ayyuka, David Umahi, na jawabi a wajen wani taro Hoto: Senator Engineer David Nweze Umahi
Source: Facebook

Ya kara da cewa lalacewar hanyoyin kwalta yawanci yana da alaka ne da rashin sa ido na gari, ba wai nau'in kayan da aka yi amfani da su ba.

Tun da farko, Umahi ya soki tsarin samar da kudade na manyan ayyuka, inda ya siffanta tsarin raba kudi na ma'aikatar kudi ta tarayya a matsayin wanda ke kawo cikas ga nasarar ma'aikatarsa.

Yayin da yake kare kasafin kudi na naira triliyan 3.4 na ma'aikatar, ministan ya bayyana cewa tsarin samar da kudaden na yanzu yana kawo cikas ga gudanar da ayyukan ma'aikatar yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta zauna, ana son gwamnati ta cire tallafin wutar lantarki

Minista Umahi ya yi kira ga Musulmai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan ayyuka, David Umahi, ya yi muhimmin kira ga al'ummar Musulmai na Najeriya.

David Umahi ya buƙaci al'ummar Musulmi da su ci gaba da yi wa Tinubu addu’a da kuma ba shi cikakken goyon baya.

Ministan ya nemi a yi wa shugaban kasar addu'o'in ne da nuna goyon baya domin ya sake samun nasarar lashe zabe a shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng