Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Alhazai bayan Sheikh Pakistan

Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Alhazai bayan Sheikh Pakistan

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Ismaila Abba Yusuf a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa a yau Laraba, 11 ga Fabrairun 2026
  • Sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ya nuna cewa sabon shugaban zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Sale Usman da ya jagoranci hukumar a baya
  • Mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana cewa Bola Tinubu ya tura takarda ga majalisar dattawa domin tantance sabon shugaban da ya nada

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon shugaba a hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) bayan Farfesa Abdullahi Sale Usman ya yi murabus.

A sanarwar da Legit Hausa ta samu daga fadar shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada Ismail Abba Yusuf a matsayin wanda zai jagoranci hukumar a yanzu.

Kara karanta wannan

IFAD: Ministan Tinubu ya samu gagarumar nasara, an ba shi babban mukami a duniya

Sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa
Sabon shugaban hukumar NAHCON, Ismaila Abba Yusuf. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa shugaban zai fara aiki da zarar majalisar dattawa ta kammala tantance shi.

An nada sabon shugaban NAHCON

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON).

Naɗin na jiran amincewar majalisar dattawa kamar yadda sashe na 3(2) na dokar NAHCON ta 2026 ya tanada.

Shugaba Tinubu ya aike da wasiƙa a yau ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

A wasikar, Tinubu ya nemi a gaggauta tantancewa da tabbatar da Ambasada Yusuf domin maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman.

Farfesa Abdullahi Usman ya yi murabus a wannan makon bayan kusan watanni 14 a kan muƙamin.

Tsohon shugaban NAHCON
Sheikh Abdullahi Sale Usman da ya rike NAHCON a baya. Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Waye Ismail Abba Yusuf?

Hukumar alhazai ta kasa ta wallafa a Facebook cewa Ambasada Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa ya riƙe muƙamin Jakadan na musamman na Najeriya a Türkiyya daga shekarar 2021 zuwa 2024.

Kara karanta wannan

Matsalolin da za a iya fuskanta hajjin bana bayan Sheikh Pakistan ya y murabus

Aikin da NAHCON za ta tunkara

A halin yanzu, ana ganin cewa dole sabon shugaban hukumar zai fara kokarin samar da hadin kai a NAHCON, lura da cewa murabus din tsohon shugaban zai iya haifar da gibi.

Haka zalika ana ganin cewa ya karbi shugabanci a kurarren lokaci, dole hukumar ta tashi ta yi aiki tukuru wajen kammala dukkan ayyukan da suka kamata domin yin jigilar alhazai lafiya.

'Yan Najeriya da dama za su zuba ido su ga irin sauye-sayen da zai kawo a hukumar NAHCON lura da kwarewar diflomasiyya da fadar shugaban kasa ta ce yana da shi.

Dalilin murabus din Sheikh Pakistan

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar alhazai ta kasa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman da aka fi sani da Pakistan ya yi magana kan ajiye aiki da ya yi.

Sheikh Pakistan ya bayyana cewa ya ajiye aiki a hukumar NAHCON ne saboda dalilai na shi na karan kai ba wani ne ya tilasta masa ya yi murabus ba.

Baya ga haka, malamin ya yi godiya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa damar da ya ba shi wajen jagorantar hukumar alhazai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng