Rana Ta Baci: An Kama 'Yan Fashi Dauke da Kayan Sata na Miliyoyin Naira a Jigawa
- Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta kama mutane bakwai da ake zargi da fashi da makami da satar shanu a wasu samame
- An samu nasarar kwato injinan POS, wayoyi, katunan ATM, shanu, da tumaki daga hannun wadanda ake zargin a fadin jihar
- Kwamishinan yan sandan jihar ya yaba wa jami'ansa tare da kira ga jama'a da su bayar da hadin kai domin tabbatar da tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Rundunar ƴan sandan Jigawa ta kama mutane biyar da ake zargi da fashi da makami da wasu barayin shanu biyu a jihar.
Kakakin rundunar, SP Shi’isu Adam, ya tabbatar da cewa an ƙwato kayayyakin sata na miliyoyin Naira a ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar.

Source: Facebook
An gudanar da waɗannan samamen ne ta hanyar amfani da dabarun tsaro tare da sa hannun al'umma da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro in ji rahoton Punch.
An kama 'yan fashi a Taura da Ringim
A ranar 6 ga Fabrairu, 2026, jami'an tsaro suka kama Ahmed Musa mai shekara 22 a Taura tare da wayoyi da katunan ATM da kuma kuɗi.
Hukumar tana zargin Ahmed Musa da kasancewa ɗan wata ƙungiyar 'yan fashi da makami da ke addabar garin Taura da kuma makwabtan garin.
Haka kuma, jami'ai daga Ringim sun kama Abdullahi Danladi da wasu mutum uku, inda aka ƙwato injinan POS guda biyu da wasu na'urori.
Gaba ɗaya, ƴan sanda sun samu nasarar ƙwato injinan POS guda biyu, wayoyi biyar, katunan ATM guda biyar, da kuma tsabar kudi N940,000 daga hannun waɗanda ake zargin.
Murƙushe masu satar shanu a Birnin Kudu
Rundunar ta kuma kama Isa Alhaji Sabo mai shekara 20, tare da shanu guda bakwai waɗanda aka sato daga garuruwan Rangwam da Alwashi.
Isa Sabo ya amince cewa ya haɗa baki da wasu mutane biyu, inda jami'an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran abokan burmin nasa.
A sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce an kama Adamu Babare mai shekara 24 bayan ya saci dabbobi guda 11, inda aka ƙwato guda tara.
Sanarwar ta ce An kama Adamu ne a ranar 3 ga Fabrairu, inda yake kokarin sayar da raguna tara cikin 11 da ya sata a gundumasr Sundimina, amma an gano ya riga ya sayar da biyu.

Source: Facebook
Matakin da 'yan sanda suka dauka
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Dahiru Muhammad, ya yaba wa jami'an bisa jajircewarsu, sannan ya ba wa jama'a tabbacin ci gaba da yaƙi da miyagu.
Ya jaddada cewa dukkan waɗanda aka kama za su fuskanci shari'a bayan an kammala bincike a sashen binciken manyan laifuka na rundunar dake jihar.
Daga ƙarshe, rundunar ta yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da ba da bayanan sirri akan lokaci domin tabbatar da zaman lafiya.
Karanta sanarwar a nan kasa:
An kama tarin 'yan fashi a Jigawa
A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sandan Jigawa ta ce ta kama mutane da dama da ake zargi da fashi da makami a ƙananan hukumomin jihar.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta nuna cewa wadanda aka kaman, ana zargin suna yin sace sace da kuma barazanar kisan kai ga al'ummar Jigawa.
'Yan sanda daga ƙananan hukumomin Birniwa, Malam Madori da Babura ne suka haɗaka kai da mafarauta wajen kama barayin da suka fitini masarautar Hadeja.
Asali: Legit.ng


