An Kama Tarin Yan Fashi da Suka Addabi Kananan Hukumomin Jigawa

An Kama Tarin Yan Fashi da Suka Addabi Kananan Hukumomin Jigawa

  • Rundunar yan sanda a Jigawa sun samu nasara kan tarin yan fashi a ƙananan hukumomin jihar daban daban
  • Bayan sata, wasu daga cikin yan fashin da aka kama ana zargin sun yi barazanar kisa ga mutane a jihar Jigawa
  • Kakakin yan sandan jihar Jigawa ya bayyana matakin da za a dauka a kan su bayan an kammala bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Yan sanda sun kama mutane da dama da ake zargi da fashi da makami a ƙananan hukumomin jihar.

Ana zargin mutanen da aka kama ne da sace sace da kuma barazanar kisan kai ga al'ummar Jigawa.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu bayan sace jariri dan kwanaki 7 a gidan suna

Yan sanda
An kama tarin yan fashi a Jigawa. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Kakakin yan sandan jihar Jigawa, Lawal Shiisu Adam ne ya bayyanawa Legit yadda aka kama yan fashi da makamin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama yan fashi a kananan hukumomin Jigawa

1. Karamar hukumar Gwaram

Yan sanda sun cafke mutane biyu da ake zargi da fashi da makami a karamar hukumar Gwaram.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen sun shiga wani gida da dare suka bukaci a ba su buhun riɗi ko su yi kisan kai kuma sun yi satar waya a wani gida.

2. Ƙaramar hukumar Hadeja

Yan sanda daga ƙananan hukumomin Birniwa, Malam Madori da Babura sun haɗaka da yan farauta wajen kama barayin shanu da suka fitini masarautar Hadeja.

An kama mutane 13 da ake zargi tare da shanu bakwai da ake kyautata zaton na sata ne a wajensu.

3. Karamar hukumar Malam Madori

Kara karanta wannan

An kama dan fashin da ya addabi mutane, ya tona inda ya sayo makamai

Yan sandan sun kama wani matashi da ake zargi ta satar babur, haka zalika an zargi matashin da damfarar wani mutum babur da kudin ta ya kai N300,000.

4. Karamar hukumar Kazaure

Rundunar yan sanda ta samu korafi daga wani mutum da aka sace masa babur a yankin Gidan Ruwa a karamar hukumar Kazaure.

Biyo bayan samame, yan sanda sun kama mutum biyu kuma sun amince da cewa su suka sace babur din.

5. Karamar Hukumar Dutse

Yan sanda sun kama wani mutum da ya yi yunkurin satar batirin da ake amfani da shi wajen samar da wuta ta hasken rana a unguwar Fatara da ke Dutse.

6. Karamar hukumar Gwiwa

Yan sanda sun kama mutane biyu da suka tare mai acaba suka masa barazanar kisa suka kwace masa babur a karamar hukumar Gwiwa.

Rundunar yan sanda ta ce za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban alkali da zarar an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Mota ta markaɗe yan Maulidi, wasu sun rasu, da dama sun samu raunuka

Ana kama dan fashi a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Jigawa ta sanar da cafke wani babban dan fashi da makami.

Wanda ake zargin mai suna Buhari Ya'u ya jagoranci fashi da makami a ƙananan hukumomin jihar Jigawa kuma an kama shi ne a jihar Benue.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng