Tinubu ko Atiku: Sheikh Jingir Ya Fayyace Wanda zai Zaba a 2027

Tinubu ko Atiku: Sheikh Jingir Ya Fayyace Wanda zai Zaba a 2027

  • Shugaban Izala na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zabinsa a zaben 2027
  • Shehin malamin ya ce kungiyar Izala mai hedkwata a Jos ba ta saba alkawari, kuma ta riga ta yi niyyar goyon bayan Tinubu da Kashim Shettima
  • Ya kuma karyata jita-jitar rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa, yana mai cewa alakar su na tafiya lafiya kamar yadda ake so

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato – Shugaban majalisar malaman kungiyar Jibwis, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne zabinsu a babban zaben 2027.

Sheikh Jingir ya bayyana hakan ne yayin taron kara wa juna sani na shekarar 2026 da kungiyar Izala ta shirya a birnin Jos, inda ya yi magana kan matsayarsa game da siyasar kasa da zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An ba Shugaba Tinubu mafita kan yadda zai yi da Kashim Shettima

Sheikh Sani Jingir da Bola Tinubu
Sheikh Sani Yahaya Jingir a hagu, Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Hamza Muhammad Sani
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Sheikh Jingir ya yi ne a wani bidiyo da jami'in yada labaran Jibwis, Ibrahim Maina Muhammad ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Sharadin Jingir kan zaben Tinubu

Sheikh Jingir ya ce ya yanke shawarar tsayawa tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu kamar yadda ya yi a zaben da aka yi a 2023.

Shugaban kungiyar Jibwis ya bayyana cewa a zaben da ya gabata, ya goyi bayan Bola Tinubu ne bisa alkawarin kawo sauyi da inganta rayuwar al’umma.

Malamin ya bayyana cewa sharadinsa shi ne cika alkawari da kuma mayar da alheri, wanda hakan ne za su sanya shi sake zaben Bola Tinubu.

Ya kuma yi kira ga gwamnoni da ministoci su yi aiki, yana nuni da cewa wasu na gaza aiki yadda ya kamata domin suna so a zagi shugaban kasa Tinubu.

Dangantakar Tinubu da Shettima

Shehin malamin ya kuma yi magana kan jita-jitar da ke yawo game da rashin jituwa tsakanin shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure: Tsohon dan majalisa ya shirya kara wa da Tinubu, zai nemi takara

Shugaban Izala ya ce irin wadannan jita-jita ba su da tushe balle makama, domin babu wata alama da ke nuna sabani a tsakaninsu.

Aminiya ta rahoto cewa ya tambayi jama’a ko sun taba jin shugaba Tinubu ya zagi Shettima, ko kuma Shettima ya taba sukar shugaba Bola Tinubu.

Shugaban Malaman Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir
Sheikh Sani Yahaya Jingir yayin wani wa'azi a Jos. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Source: Facebook

Sheikh Jingir ya yi fatan Tinubu da Shettima su kammala wa’adinsu lafiya, kuma idan Allah ya so, za su sake samun nasara a zaben 2027.

A jawabin nasa, shugaban Izala ya shawarci shugaba Tinubu da ya yi adalci ga kowane dan Najeriya ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.

Solomon Dalung ya caccaki Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung ya caccaki gwamnatin APC karkashin Bola Ahmed Tinubu.

Dalung ya bayyana cewa 'yan APC suna da manyan mutane da suka tsaya domin kalubalantar APC da Tinubu a zaben shekarar 2027.

Tsohon ministan ya ce ADC ta shirya domin gudanar da zaben fitar da gwani mai tsafta kuma za su goyi bayan duk wanda ya yi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng