Rahoto: 'Yan Najeriya 43,000 Ke Fama da Cizon Maciji duk Shekara

Rahoto: 'Yan Najeriya 43,000 Ke Fama da Cizon Maciji duk Shekara

  • Akalla ‘yan Najeriya sama da 43,000 ne ke fuskantar cizon maciji a duk shekara, kuma sukan sha wahala kafin samun magani
  • Rahoto ya bayyana irin matsalar da fannin lafiyar Najeriya ke fuskanta wajen samun maganin kasha dafin maciji
  • A bangare guda, masana sun bayyana inda matsalar ta ke da kuma hanyoyin magance matsalar cikin gaggawa idan an natsu

Najeriya - Najeriya na fuskantar wata matsalar gaggawa ta lafiyar jama’a yayin da masana lafiya ke gargadin cewa yawan wadanda maciji ke cizo kiyasin kai 43,000 a shekara.

Hakazalika, sun bayyana cewa, hakan na ci gaba da cika asibitoci da majinyata da karancin maganin kashe dafin maciji.

Masana sun ce wadanda abin ya same su suna biyan har zuwa N250,000 a kowacce allurer magance dafin.

Matsalar cizon maciji a Najeriya
Matsalar cizon maciji a Najeriya da mafita daga masana | VCG/Getty
Source: Getty Images

Sai dai, wannan yawan kudin ya haura abin da mafi yawancin manoma a karkara za su iya biya domin samun waraka da cizon da ka iya kisa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadada shirin tallafawa mata zuwa mutum miliyan 25

Rasuwar wata matashiyar mawakiya, Ifunanya Nwangene ya ƙara janyo hankalin jama’a kan bukatar gaggawa daga gwamnati don ta rage kudin allurer da kuma bunkasa kera maganin a cikin gida.

Bukatar gaggawa daga gwamnati

Masana lafiya sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta sanya kaimin samar da maganin kashe dafin maciji, tare da rarraba shi a duk asibitocin kasar.

Sun ce rashin wadatar maganin na ci gaba da haddasa mutuwar da za a iya kaucewa kamar yadda ake magancewa a wasu kasashen duniya.

A cewar rahoton PUNCH, banda karancin maganin, ana tilastawa wadanda abin ya shafa biyan tsakanin N180,000 zuwa N250,000 a kowacce allura.

A bangare guda, wannan kudi ya yi daidai da kudin shiga na watanni akalla hudu ga wadanda ke samun mafi karancin albashi na N70,000.

Masu bincike sun lura cewa raunin tsarin kiwon lafiya, karancin kayayyakin more rayuwa, da rashin maganin kashe dafin maciji sun bar 50% cikin dari na cibiyoyin lafiya cikin yanayin rashin iya maganin cizon maciji.

Kiran samar da magani a gida da rage kudin sa

Masana sun bukaci gwamnati da ta:

Kara karanta wannan

Bello Turji ya saki tsohon dan bindiga Lankai, ya tara jama'a ya yi jawabi

  • Rage kudin maganin kashe dafin maciji.
  • Shigo da mai arha daga kasashen waje.
  • Bunkasa kera maganin a cikin gida.
Matsalar da ake fuskanta a Najeriya da macizai
Wannan hoto ne da ke nuna halittar maciji a matsayin misali | Hoto: Vinicius Fonseca/Getty
Source: Getty Images

Sun jaddada cewa maganin ya kamata ya kasance kyauta a duk cibiyoyin lafiya na farko a fadin Najeriya.

Karancin maganin kasashen duniya

Dr. Nicholas Amani, Daraktan Asibitin Cizon Maciji da Cibiyar Bincike a Kaltungo, Jihar Gombe, ya bayyana maganin kashe dafin maciji a matsayin abu mai wuyar samu a duniya.

Ya ce:

“Gaskiyar magana ita ce, maganin kashe dafin maciji abu ne mai kalilan a duniya baki daya. Dalilin shi ne cizon maciji ya fi shafar marasa galihu, manoma, da masu zama a karkara, mutanen da ba su da karfin magana.”

Ya kara da cewa har yanzu asibitocin musamman ba su da wadataccen magani, kuma kokarin gwamnati na magance matsalar na ci gaba.

Farfesa Patricia Lar, masanin kwayoyin cuta a Jami’ar Jos, ta yi suka kan dogaro da Najeriya ke yi kan shigo da magani daga Indiya, China, da Birtaniya.

Yadda ake hada maganin dafin maciji

Kara karanta wannan

Kwamitin Sarkin Musulmi ya yi magana kan duba watan Ramadan 2026

A wani labarin, masana kimiyya sun gano wata gagarumar dama a fannin lafiya daga wani mutum dan kasar Amurka, Tim Friede, wanda ya shafe fiye da shekaru 18 yana shan gubar macizai.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Tim Friede ya shafe shekaru yana shan gubar ne domin ya kare jikinsa daga cizon maciji.

Rahoton New York Times ya nuna cewa Friede ya ce ya fara wannan aikin ne domin kare kansa yayin da yake kula da macizai, amma daga baya ya juya hakan zuwa wani abu na daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng