Bayan Abba Ya Shiga APC, Shugaba Tinubu Zai Yi Aikin Titin Naira Biliyan 19 a Kano

Bayan Abba Ya Shiga APC, Shugaba Tinubu Zai Yi Aikin Titin Naira Biliyan 19 a Kano

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta amince da Naira biliyan 19 domin ci gaba da aikin titin Kano zuwa Dayi wanda ya kai nisan kilomita 100
  • Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa aikin zai saukaka safarar amfanin gona da kuma bunkasa tattalin arzikin kananan hukumomin yankin
  • Wannan ci gaba na zuwa 'yan kwanaki bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince a fitar da Naira biliyan 19 domin ci gaba da aikin titin Kano–Gwarzo–Dayi.

Wannan amincewa ta biyo bayan ganawar da Barau ya yi da mataimakin shugaban kamfanin CGC Nigeria Limited, Lv Haiming, a birnin Abuja domin warware matsalolin da suka dakatar da aikin.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Tinubu ya sanya labule da Gwamna Uba Sani a Aso Rock Villa

Gwamnatin tarayya ta amince da kashe N19bn don aikin titi a Kano
Gwamna Abba Yusuf tare da Shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Bola Tinubu zai gina titin N19bn a Kano

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a yau Juma'a, inda ya ce wannan matakin ya yi daidai da tsarin "Renewed Hope" na Shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa an kammala duk wani shirye-shirye, kuma an riga an bai wa kamfanin kwangilar domin komawa bakin aiki cikin gaggawa don kammala wannan muhimmin titi.

Sanata Barau ya bayyana titin na Kano–Gwarzo–Dayi a matsayin wata hanya mai muhimmanci da ta haɗa garuruwa da dama a Jihar Kano da sauran jihohi maƙwabta.

Ya bayyana cewa:

“Ina farin cikin sanar da cewa an kammala dukkan tsare-tsare, kuma an amince da fitar da Naira biliyan 19 domin aiwatar da aikin titin Kano–Gwarzo–Dayi.”

Ya ƙara da cewa:

“Wannan hanyar za ta ƙarfafa alaƙa, ta haɓaka harkokin tattalin arziki, sannan ta inganta jin daɗin rayuwar mutanenmu dake wadannan yankunan baki ɗaya.”

Tsaikon da aka samu a aikin titin

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da aikin maida titin zuwa mai hannu biyu ne tun a ranar 11 ga watan Yunin 2021 akan kuɗi Naira biliyan 62.7.

Sai dai abin takaici, aikin ya tsaya cik kusan shekaru uku da suka gabata, lamarin da ya janyo wa matafiya da manoma dake safarar amfanin gona wahalhalu.

Al'ummomin yankin da abin ya shafa sun sha yin barazanar mamaye majalisar dokoki ta kasa sakamakon rashin sakin kuɗin kammala aikin da gwamnatin baya ta yi.

Titin, wanda tsawonsa ya kai kusan kilomita 100, an tsara shi ne domin sauƙaƙa sufuri da kuma kai amfanin gona daga karkara zuwa manyan kasuwannin jihohin Arewa.

Sanata Barau Jibrin ya ce aikin titin zai kawo cigaban tattalin arziki a ayyukan da abin ya shafa.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanat Barau Jibrin yana jagorantar zaman majalisa. Hoto: @barauijibrin
Source: Facebook

Jajircewar Sanata Barau ga bukatun jama'a

Sanata Barau ya sake tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatin Tinubu tana da kyakkyawar niyya wajen kammala manyan ayyukan da suka shafi rayuwar ƴan ƙasa kai-tsaye.

Ya ce an riga an tura ƴan kwangilar zuwa wajen aiki, kuma za a tabbatar da cewa an yi aiki mai inganci wanda zai dore na tsawon lokaci.

Wannan sanarwa ta janyo nishaɗi ga jama'ar Gwarzo da maƙwabta, waɗanda ke ganin wannan mataki a matsayin amsar addu'o'insu na tsawon lokaci game da wannan titi.

Kara karanta wannan

Bayan jiran kusan shekaru 50, Uba Sani ya kaddamar da hanya a kauyukan Kaduna

Gwamnan Kano ya shiga jam'iyyar APC

A wani labari, mun ruwaito cewa, bayan tsawon lokaci ana tirka-tirka a siyasar jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ne suka karbi Gwamna Abba.

Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan Abba ya mika takardar ficewa daga jam'iyyar NNPP a mazabarsa da ke karamar hukumar Gwale a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com