Gwamnatin Buhari ta ji kukan jama’a, ta fara gina titin da ya hada mutanen Kano da Katsina

Gwamnatin Buhari ta ji kukan jama’a, ta fara gina titin da ya hada mutanen Kano da Katsina

An kaddamar da aikin gina titin Gwarzo (Kano) zuwa Dayi (Katsina)

Za a kashe Naira Biliyan 60 wajen wannan hanya mai kilomita 90.65

Ana sa ran gama aikin a 2023, kuma ayi shekara 20 ana morar titin

Gwamnatin tarayya ta fara aikin gina babban titin Kano-Gwarzo-Dayi wanda zai hada jihohin Kano da Katsina, jaridar The Nation ta bayyana haka.

A ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, 2021, aka kaddamar da shirin gina wannan titi mai tsawon kilomita 90.65, ana sa rai za a kammala a shekaru biyu.

Kamar yadda darektan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar ayyuka da gidaje na tarayya, Boade Akinola, ya fada, aikin zai ci Naira biliyan 62.711.

KU KARANTA: Idan na bar Aso Villa, gona zan koma - Buhari

Boade Akinola ya fitar da jawabi inda ya hakaito sakataren din-din-din na ma’aikatar, Babangida Hussaini, ya na cewa CGC Nigeria Ltd aka ba kwangilar.

Darektar da ke kula da manyan hanyoyin gwamnatin tarayya na Arewa maso yamma, Folorunsho Esan ta wakilci Babangida Hussaini wajen bikin soma aikin.

A Nuwamban 2020 ne majalisar zartarwa ta kasa ta amince da wannan kwamgila. A ranar 1 ga watan Disamba, 2020 ne aka bada kwangilar wannan aikin.

Rahoton ya ce a wannan hanya mai sahu biyu, za a samu gadoji uku, da kuma karin kafafu a kan titin.

KU KARANTA: Buhari ya bayyana hikimar nadin mukaman da yake yi

Wani titi a Najeriya
Wani titi a Najeriya Hoto: www.radionigeria.gov.ng
Asali: UGC

Za a ja layin tafiya, da allon maleji da duk wasu alamomi a kan hanyar. Hussaini ya ce za ayi shekaru 20 ana morar wannan titi idan an kammala aikin.

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya yaba da wannan aikin, ya ce titin zai taimakawa ‘Yan Kano, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi.

Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da na Karaye, Dr. Alhaji Ibrahim Abubakar, sun halarci bikin kaddamar da aikin.

A jiya an ji cewa Sunrise Power Transmission Company of Nigeria ya kai karar Gwamnatin Tarayya a kan aikin Mambilla, ya na neman a biya sa N200bn.

Wannan kamfani ya dauki hayar Femi Falana zuwa kotun Duniya. Hakan ya sa ake ganin shirin samar da karin wutan lantarki na 3500MW ya na samun cikas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel