Gwamna Ya Ba da Umarni da Aka Shirya Mamaye Fadar Sarki domin Kwace Iko

Gwamna Ya Ba da Umarni da Aka Shirya Mamaye Fadar Sarki domin Kwace Iko

  • Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya gargadi duk masu shirin kutsawa ko karbe ikon fadar Ikirun Sarki ba bisa ka’ida ba
  • Gwamnan ya umurci jami’an tsaro da su gaggauta kewaye wa da kare fadar domin hana duk wani tayar da hankali
  • Adeleke ya ce fadar Ikirun za ta ci gaba da kasancewa a kulle har sai kotu ta kammala shari’ar sarautar Akirun

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi gargadi mai tsauri ga duk masu shirin kutsawa ko karbe ikon Fadar Ikirun

Gwamnan Osun ya ba da umurni ga hukumomin tsaro da su gaggauta daukar matakai domin kare fadar daga kai mata farmaki.

Gwamna ya umarci mamaye fada da ake shirin kutsawa
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun. Hoto: Governor Ademola Adeleke.
Source: Twitter

Gwamna ya gargadi masu neman ta da rigima

Hakan na cikin wata sanarwa da kakakinsa, Mallam Olawale Rasheed, ya fitar a jiya Alhamis 5 ga watan Fabrairun 2026, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Bayan kyautar N100m, gwamna Abba ya dauki matakai a kan gobara a kasuwar Kano

Gwamnan ya bayyana cewa duk wani basarake ko mai sarauta da aka samu yana da hannu a wannan yunkuri za a dauke shi a matsayin mai laifi kuma za a hukunta shi bisa doka.

Adeleke ya ce fadar Ikirun za ta ci gaba da kasancewa a kulle har sai an kammala shari’ar da ke gaban kotu kan kujerar Akirun.

Ya ce:

"Duk wani yunkuri na tayar da zaune tsaye a Ikirun ba za a lamunta ba. Batun sarautar Akirun na gaban kotu, kuma har sai an yanke hukunci, ba za mu amince da daukar doka a hannu ba.”
Ana shirin mamaye fadar Sarki da ake rigima
Taswirar jihar Osun da ke rigimar sarauta. Hoto: Legit.
Source: Original

Umarnin da Tinubu ya ba Gwamna

Gwamnan ya kara da cewa umarnin shugaban kasa ne ya dawo da zaman lafiya a Ikirun, kuma sai da wani sabon umarninsa ne kawai za a iya sake bude fadar.

A cewarsa, bude fadar da aka yi kwanan nan ba don wani aiki ba ne face domin tsaftace muhalli da gyaran ginin, domin kiyaye muhimmin kayan al’adar gargajiya.

Gwamna Adeleke ya ce:

“Ina umartar hukumomin tsaro da su kewaye fadar tare da hana duk wani yunkuri na karbe ta ba bisa ka’ida ba. Dole ne a dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a Ikirun.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara bayan kashe Musulmai sama da 100

Gwamnan ya nanata kudurin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda a dukkan sassan jihar Osun baki daya.

Daga bisani, gwamna ya bukaci al'umma da su ci gaba da ba su hadin kai domin tabbatar da dorewar zaman lafiya wanda shi ne babban burinsa a jihar.

Matashi ya rasa ransa bayan farmakin liman

Mun ba ku labarin cewa wani mummunan lamari ya faru a masallaci inda aka lakadawa wani mai ibada duka har ya mutu a wurin bautar Ubangiji.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya tayar da husuma yayin hudubar liman, inda ya yi yunkurin kai masa hari, lamarin da ya haddasa rikici.

‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin, sun ce mutuwar ta faru a kusa da masallacin, yayin da ake ci gaba da bincike.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.