Bauchi: NEDC Ta Kawata Kabarin Tafawa Balewa a Gagarumin Gyara da Ta Yi
- Hukumar NEDC ta kammala gyaran kabarin Firaministan farko na Najeriya, Sir Abubakar Tafawa Balewa, domin kare tarihinsa da inganta wurin
- Karamin ministan raya yankuna na kasa, Uba Maigari Ahmadu, ya jagoranci hukumar NEDC wajen duba aikin da aka yi a wurin kabarin
- Gwamnatin Jihar Bauchi ta jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi domin bunkasa ci gaba da walwalar jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Bauchi – Hukumar NEDC ta Arewa maso Gabas ta kammala gyaran kabarin Firaministan farko na Najeriya, Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa, da ke Jihar Bauchi.
An kaddamar da aikin ne a wani bangare na kokarin kare tarihin kasa tare da inganta wuraren yawon bude ido da ake da su.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa Karamin ministan raya yankuna, Uba Maigari Ahmadu ya jagoranci shugabanni da ma’aikatan hukumar NEDC domin duba wurin.
Ayyukan gyaran kabarin Tafawa Balewa
Rahotanni sun nuna cewa Uba Maigari Ahmadu ya bayyana cewa aikin gyaran da NEDC ta yi ya shafi muhimman sassan wajen da kabarin ya ke.
Ya ce an gyara gidan tarihin gaba daya, dakin karatu, kabarin Firaministan, wajen karbar baki, da kuma ban-daki na maza da mata domin saukaka wa masu ziyara.
A cewarsa, an tsara wannan aikin ne domin tabbatar da cewa tarihin Firaministan farko na Najeriya bai gushe ba, tare da bai wa jama’a damar ziyarta cikin sauki da tsari.
Manufar NEDC da muhimmancin tarihi
Karamin ministan ya jaddada cewa hukumar NEDC ta dauki aikin a matsayin wani muhimmin al'amari na kare tarihin kasa da jihar Bauchi.
Ya ce Sir Abubakar Tafawa Balewa na daga cikin manyan jagororin da suka assasa Najeriya, don haka wajibi ne a kula da wuraren da ke dauke da tarihinsa.

Source: Twitter
Haka kuma ya bayyana cewa gyaran wurin zai taimaka wajen bunkasa yawon bude ido da kuma samar da damar sanin tarihi ga dalibai da masu bincike.
Maganar Gwamnan jihar Bauchi
A wani bangare na ziyarar, Uba Maigari Ahmadu tare da shugabannin NEDC sun kai ziyarar girmamawa ga Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana bukatar kara dankon hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi domin hanzarta ci gaba da inganta rayuwar al’umma.
The Sun ta rahoto ya bayyana NEDC a matsayin alamar hadin gwiwa da zumunci da ke kara kulla alaka tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin yankin.
Haka kuma ya jinjina wa shugaban NEDC, Mohammed Goni Alkali, bisa hangen nesa, jajircewa da iya aiwatar da ayyuka masu kyau.
Za a ba malamai alawus a Bauchi
A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara ba malaman addini alawus.
Bala Mohammed ya bayyana haka ne yayin wani taro a gidan gwamnatin Bauchi, inda ya ce shirin zai shafi malaman addinin Musulunci da Kirista.
Gwamnatin Bauchi ta bayyana cewa an kawo shirin ne domin tallafa wa jagororin addini su samu damar jagorantar ayyuka cikin kwanciyar hankali.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

