An kwatanta shugaba Buhari da Tafawa Balewa a siyasar zamunna

An kwatanta shugaba Buhari da Tafawa Balewa a siyasar zamunna

- Muhammadu Buhari na da irin halayen firayem minista na farko na Najeriya

- Buhari na da sauki kai sannan kuma mutumin mutane ne

- Don haka yakamata mu sake zaben shi a 2019 don ya cigaba da aiyukan alheri

An kwatanta shugaba Buhari da Tafawa Balewa a siyasar zamunna

An kwatanta shugaba Buhari da Tafawa Balewa a siyasar zamunna
Source: Twitter

Muhammadu Buhari yana da irin halayen firayem minista na farko na Najeriya, Marigayi Abubakar Tafawa Balewa.

Mista Okihere, ya bayyana hakan a garin Bauchi a yayin da shi da yan kungiyar shi suka ziyarci kabarin Marigayi Abubakar Tafawa Balewa.

"Abinda muka gane yanzu shine kamanceceniyar halayyar nagartar Marigayi Abubakar Tafawa Balewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

"Suna da kama a kwatance; Buhari mutum ne mai saukin kai kuma mutumin mutane ne. Abinda kuka karanta na takaitaccen tarihin rayuwar Tafawa Balewa da nagartar shi da halayyar shi sune muke gani a shugaban kasa Muhammadu Buhari," yace.

Yayi kira ga yan Najeriya dasu sake zabar Buhari a zabe mai zuwa domin bashi damar cigaba da aiyukan alheri da yake yi.

DUBA WANNAN: Lokutan da jiragen Kaduna-Abuja ke tashi daga tashoshin IDU-Kubwa-Rigasa (III)

"Shuwagabannin mu, shugaban kasa Muhammadu Buhari, shuwagabannin jam'iyyar APC da sauran shuwagabanni a kasa Najeriya yakamata su dawo a 2019 don karasa aiyukan habaka tattalin arzikin da suke yi. Masu zabe basu da wani zabi d ya wuce su goyi bayan Buhari da gwamnonin shi, " inji shi.

Kungiyar tsintsiyar kungiya ce ta goyon bayan APC, wacce ta hada da mutane da yawa ba wai yan jarida kadai ba.

Kungiyar aiyukan ta sun hada da kawo cigaban nagartacciyar siyasar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari da cigaba gwamnoni.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel