Shaidar EFCC Ta Yi Bayani kan Alakar Yahaya Bello da Zargin Almundahar N80bn

Shaidar EFCC Ta Yi Bayani kan Alakar Yahaya Bello da Zargin Almundahar N80bn

  • Lauyan Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi ya ce shari’ar da ake yi da mai gidansa, siyasa ce tsura ba wani abu ba
  • A shari'ar da ake yi da EFCC, shaida daga banki ta ce sunan Yahaya Bello bai bayyana a muhimman takardu da ake zargi ba
  • Alkali ya dage shari’ar zuwa 5 ga Fabrairu 2026 domin ci gaba da sauraron shaidu a kan zargin tsohon gwamnan da wawure kudin talakawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Joseph Daudu, Babban Lauya a Najeriya mai wakiltar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi magana a kan shari'a da maigidansa.

Ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja cewa shari’ar da ake yi wa wanda yake karewa ba ta da alaƙa da almundahanar kuɗi, illa dai ana tafiyar da ita ne bisa dalilan siyasa.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPCL ya tona abubuwan da suka faru da matatun gwamnati

Lauyan Yahaya Bello ya yi zargin siyasa ce ta jawo shari'a da mai gidansa
Yahaya Bello a kotu a shari'arsa da EFCC Hoto: Economic and Finacial Crimes Commission
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa lauyan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairu, 2026 a gaban kotu tare da tambayoyi ga Olomotane Egoro, wacce jami’ar kula da bin ƙa’idoji ne a Bankin Access Plc.

Lauya ya kare Yahaya Bello a kotu

Channels TV ta wallafa cewa da ya ke amsa tambayoyin lauyan Yahaya Bello, shaidan EFCC Olomotane Egoro, ta ce shugabannin ƙananan hukumomi ne suka bayar da kwangilolin da ake takaddama a kansu.

Shaidar ta kuma bayyana cewa sunan Yahaya Bello bai bayyana a ko’ina cikin takardar shaidar dangane da mu’amalolin kuɗin da ake bincike a kai ba.

Shaidan EFCC ya ce babu sunan Yahaya Bello a zargin badakala
Yahaya Bello, tsohon gwamnan Kogi, ofishin EFCC a Abuja Hoto: Alhaji Yahaya Bello/Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Ta ce:

“Sunan ‘Yahaya Bello’ bai bayyana ko a matsayin mai aikawa ko mai karɓa ba."

Shaidar EFCC ta yi magana kan Yahaya Bello

Egoro ta ƙara da cewa bayanan da ke cikin shaidar kotu ta 33(11), waɗanda ke nuna mu’amaloli tsakanin ƙananan hukumomi da kamfanin Keyless Nature Limited, sun yi kama da mu’amalolin banki na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Dalung ya kalubalanci kama Malami da DSS ta yi

Shaidar ta kuma ce kwastomomi na da ‘yancin kashe kuɗinsu yadda suka ga dama muddin babu zamba.

Game da kuɗin da aka biya wa Fayzade Business Enterprise, Egoro ta ce kuɗin da ya shigo daga ƙaramar hukumar Okene a ranar 6 ga Mayu, 2022, an biya su ne domin samar da kayan karatu.

An lissafa wasu kuɗi daga Ogorimagongo, Okehi, Omala da Yagba a matsayin kuɗin sayen kayan ilimi, na kiwon lafiya, kayan wasanni da sauran kayayyaki.

Da aka tambaye ta ko Yahaya Bello shugaban ƙaramar hukuma ne, Egoro ta ce:

“A’a, wanda ake tuhuma ba shugaban ƙaramar hukuma ba ne.”

A ƙarshe, alkali Emeka Nwite ya dage shari’ar zuwa 5 ga Fabrairu 2026 domin ci gaba da gicciye tambayoyin shaidar.

Yahaya Bello zai iya neman kujerar Natasha

A baya, mun wallafa cewa tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa ya amince da kiran da aka yi masa na tsayawa takarar Sanatan Kogi ta Tsakiya a babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun bi sawun dan kasuwar Kano, sun ɗauke shi a jihar Nasarawa

Wannan sanarwa ta fito ne a yayin wata ziyara da ya kai fadar Ohinoyin Ebira, inda ya gana da sarakunan gargajiya, malamai, shugabannin siyasa da sauran mahukunta a yankin.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa da ra’ayoyi a fagen siyasar Kogi, musamman game da wanda zai wakilci yankin Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya a zaɓen mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng