Tonon Asiri: Yadda Ɗan Najeriya Ya Damfari Baturiya $2.5m da Sunan Yariman Dubai

Tonon Asiri: Yadda Ɗan Najeriya Ya Damfari Baturiya $2.5m da Sunan Yariman Dubai

  • Wani dan Najeriya Nzube Ikeji ya yi amfani da sunan yariman Dubai na bogi wajen damfarar wata Baturiya dala miliyan biyu da rabi
  • Masu damfarar sun yi amfani da soyayyar intanet da asusun banki na karya wajen yaudarar matar, 'yar Romania kafin asirinsu ya tonu
  • Binciken OCCRP ya nuna cewa wadanda ake zargi da laifin suna da alaka da manyan yan siyasa da hamshakan yan kasuwar Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani bincike na musamman da ƙungiyar OCCRP ta gudanar ya bankaɗo yadda wata ƙungiyar masu laifi ta Najeriya ta zambaci wata mata ƴar ƙasar Romania.

Masu damfarar, ƙarƙashin jagorancin wani hamshakin matashi Nzube Ikeji, ta yi amfani da dabarun soyayyar intanet wajen tatsar matar kuɗaɗe masu yawa.

An gudanar da bincike kan yadda wani dan Najeriya ya damfari baturiya dala miliyan 2.5
Dan Najeriya, Nzube Ikeji da ake zargin ya yaudari baturiya $2.5m. Hoto: nicoletaionescu
Source: Getty Images

Yadda dan Najeriya ya yaudari baturiya

Kara karanta wannan

Abin da ya hana Epstein kasuwancin mai a Najeriya, ya shiya ganawa da Jonathan

An gudanar da damfarar ne ta hanyar nuna cewa Nzube Ikeji wani yariman Dubai ne mai suna Sheikh Hamdan Mohammed Bin Rashid Al Maktoum, in ji rahoton Premium Times.

Binciken ya nuna cewa Ikeji ya tuntuɓi matar, wadda aka sakaya sunanta da Laura, ta dandalin LinkedIn inda ya nuna sha'awar zuba jari a fannin ayyukan jin kai a kasarta.

Ya bayyana mata cewa yana son tallafa wa ƙungiyoyin jin ƙai a ƙasarta ta Romania, inda ya nemi shawararta kan waɗanda suka dace.

Daga nan ne suka fara tattaunawa ta sana'a, wadda daga baya ta rikide zuwa soyayya ta intanet har ya nemi ya aure ta.

Bayan nan ya bukaci ta biya kuɗaɗen shirye-shiryen neman aurensu, sannan ya tura ta London domin ganawa da manajansa na kuɗi.

Dabarar amfani da asusun banki ka karya

A London, Laura ta haɗu da Martins Abhulimhen, wanda ya yi ikirarin shi ne Matthew Cros, manajan kuɗi na yariman na ƙarya.

An ba ta bayanan shiga wani asusun banki na intanet wanda ke nuna tana da kuɗi har fam miliyan 202 a cikinsa.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Atiku ya yi ganawar sirri da babban Sanatan APC Abdulaziz Yari

Sai dai bincike ya nuna cewa wannan asusun na bogi ne kuma an tsara shi ne ta kwamfuta domin a yaudari baturiyar.

Don cire waɗannan kuɗaɗe, an bukaci ta fara biyan fam 7,000, inda hakan ya zama farkon kwararar kuɗaɗenta zuwa hannun ɓata-garin.

Duk lokacin da ta yi ƙoƙarin cire kuɗi, sai a bukaci ta biya ƙarin haraji, har ta kai ga ta tura sama da dala miliyan 2.5, cewar wani rahoto na jaridar The Cable.

Yadda asirin dan Najeriya ya tonu

Asirin ya tonu ne sakamakon saɓani da aka samu tsakanin mambobin ƙungiyar damfarar kan yadda za su raba kuɗaɗen da suka sace.

Ɗaya daga cikin mambobin ƙungiyar ya tuntuɓi Laura inda ya gaya mata cewa an damfare ta sama da Euro miliyan 3.

Binciken OCCRP ya gano cewa Ikeji da Abhulimhen suna da alaƙa da manyan mutane a Najeriya, ciki har da jami'an gwamnati da hamshakan ƴan kasuwa.

Hotuna sun nuna su tare da Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Godswill Akpabio, da kuma shugaban kamfanin Cubana Group, watau Obi Cubana.

Kara karanta wannan

"Ba zan zama mataimakin Atiku ko Kwankwaso ba," Obi ya fadi shirinsa kan 2027

Da aka tuntubi Nzube Henry Ikeji kan wadannan zarge zarge, sai ya ce a tuntubi lauyoyinsa.
Dan Najeriya, Nzube Ikeji da ake zargin ya yaudari baturiya $2.5m. Hoto: @afam_bu_nzubechukwu001
Source: Twitter

Martanin Nzube Ikeji kan zargin

Lokacin da OCCRP ta tuntuɓi Nzube Ikeji a gidansa dake Abuja, ya ƙi bayar da amsa kai-tsaye kan zargin da ake masa.

Ya buƙaci masu binciken su tuntuɓi lauyoyinsa, yana mai cewa:

“Zai fi kyau ku tuntuɓi tawagar lauyoyina kan waɗannan tambayoyi da ku ke yi mini.”

Hukumar ƴan sandan Birtaniya ta riga ta gano cewa "Matthew Cros" sunan bogi ne da Martins Abhulimhen yake amfani da shi.

Wannan rahoto ya janyo ce-ce-ku-ce kan yadda masu damfara ke amfani da hotunan manyan mutane domin samun kariya da kuma yaudarar baƙi.

A halin yanzu, ana jiran ganin ko hukumomin Najeriya irin su EFCC za su ɗauki mataki kan wannan babban bankaɗi na duniya.

Mutumin Najeriya ya damfari dubban mata

A wani labari, mun ruwaito cewa, wani 'dan Najeriya Ikechukwu N. ya shiga hannu a Argentina bisa zargin damfara ta yanar gizo da ya shafi dubunnan mata.

Kara karanta wannan

'Ba talauci ba ne,' Peter Obi ya fadi ainihin matsalar da ke addabar Najeriya

An cafke shi ne karkashin aikin hadin gwiwa da aka lakaba suna "Operation Jackal", wanda INTERPOL ke jagoranta domin dakile damfara.

An ce Ikechukwu da tawagarsa na yaudarar mata da kalaman soyayya har su fada tarkonsu, su karbi makudan kudi daga hannunsu, a wani salo na damfara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com