Daga Yin Soyayya Wata Mata Tayi Asarar Miliyoyin Ƙudaɗen Ta

Daga Yin Soyayya Wata Mata Tayi Asarar Miliyoyin Ƙudaɗen Ta

  • Wata mata ta faɗa tarkon ɗan damfara da sunan soyayya a yanar gizo inda tayi asarar miliyoyin kuɗaɗe
  • Saurayin yayi wa matar shigo-shigo ba zurfi inda ya sanya ta ajiye aikin da take yi ta koma bata da komai
  • Mutane masu sharhi a yanar gizo sun ƙi su tausayawa matar inda suka ce ai da gangan ta bari aka damfare ta

Wata mata ta faɗa kogin soyayya da wani mutum a yanar gizo ɗan ƙasar Kenya, sai dai ba taji da daɗi ba a ƙarshe.

Matar mai suna Sthembile Duma mai shekara 51 a duniya, jikinta ya gaya mata inda ta rasa dukkanin abinda ta mallaka saboda soyayya.

Labarin Sthembile ya ɗauki hankula a Tuwita inda mutane da dama suka nuna mabambanta ra'ayoyi. Mutane da yawa ba su tausaya mata ba bayan sun saurari gabaɗaya labarin na ta.

Kara karanta wannan

Gwamna Tambuwal Ya Bayyana Lokacin Da PDP Zata Yankewa Wike Da Ƴan G5 Hukunci

Saurayi
Daga Yin Soyayya Wata Mata Tayi Asarar Miliyoyin Ƙudaɗen Ta
Asali: UGC

@VehicleTrackerz ya sanya labarin matar wacce tayi rashin sa'a a soyayya. Sthembile tayi tunanin cewa ta samun abokin rayuwa lokacin da ta fara magana da mutumin ɗan ƙasar Kenya. Rahoton Legit.ng

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai abin takaicin shine soyayyr ta su ta zo ƙarshe inda har ta bar aikinta saboda saurayin na ta, wannan matakin da ta dauƙa na ajiye aikinta ya sanya ta rasa gidanta da kuma kuɗin fansho kimanin ₦2.2m.

Labarin ya kuma yi ƙarin haske cewa Sthembile yanzu ƙwayayen kaza huɗu kawai ta mallaka a duniya.

Mutanen da suka tofa albarkacin bakin su kan lamarin ba su nuna wani nuna tausayawar su ga matar ba. Inda da yawa ba suji kunyar bayyana cewa damfara a yanar gizo ba wani baƙon abu bane sannan sun ɗora laifin akan matar.

Wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Faɗi Gaskiya Kan Dan Takarar Da G-5 Ta Kulla Yarjejeniya da Shi

@khantiowen ya rubuta:

"Laifin ta ne."

@Marupin82983629 ya rubuta:

"Yawan shan wahalar matan Afrika ta Kudu yawan yadda za su gane abubuwa, ina nufin har sau nawa zamu gaya muku irin waɗannan sheɗanun masu ƙaryar suna soyayya da ku, kafin ku ankara sun wawushe muku kuɗaɗe?"

@fourrforty ya rubuta:

"Shin yakamata mu tausaya mata? "

Bidiyon Yadda Kare Ya Hau Sama, Ya Janyo Kusan N900k Ya Yagalgala

Karen wata mata ya janyo mata asarar maƙudan kuɗaɗe bayan ta tafi ta ɓar shi a gida shi kaɗai. Bidiyon yadda karen ya tafka wannan ta'asar ya bayyana.

Karen ya hau sama ya janyo kuɗaɗen matar daga wurin ajiyar su inda ya bi su ya yagalgala su. Hakan ya sanya matar yin nadama sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel