EFCC Ta Cafke Fitacciyar Jarumar Kannywood, Samha Inuwa, Ta Aikata Babban Zunubi

EFCC Ta Cafke Fitacciyar Jarumar Kannywood, Samha Inuwa, Ta Aikata Babban Zunubi

  • Hukumar EFCC ta cafke jarumar Kannywood Samha Inuwa a Jihar Kano bisa zargin goge majina da takardun kudin Naira a cikin wani bidiyo
  • Jarumar tana tsare a ofishin hukumar yayin da ake gudanar da bincike kafin a gurfanar da ita a gaban kotun tarayya nan kusa
  • Wannan kamu na nuna kudurin EFCC na kare darajar kudin kasar Najeriya da kuma hukunta duk wanda aka samu yana wulakanta Naira

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) reshen jihar Kano, ta cafke fitacciyar jarumar Kannywood, Samha Inuwa.

An kama jarumar ne a ranar Talata, 3 ga watan Fabrairu, 2026, bisa zargin cin zarafi da wulaƙanta takardun kuɗin Najeriya, watau Naira.

EFCC ta casfke fitacciyar jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa.
Fitacciyar jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa da EFCC ta kama. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Bidiyon Samha da ya jawo hankalin EFCC

Kara karanta wannan

Abin da Emefiele ya ce ga Buhari a takardar neman izinin sauya fasalin Naira

Wannan kamu ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, inda aka ga jarumar tana goge hancinta da kuɗin, in ji sanarwar da aka wallafa a shafin EFCC na Facebook.

A cikin bidiyon da ya sa aka cafke ta, an ga jarumar tana amfani da takardun Naira wajen goge majina daga hancinta a yayin da take zaune a cikin mota.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa wannan danyen aiki ne dake nuna rashin daraja ga ɗaya daga cikin alamomin ikon ƙasar nan.

Bayan ganin bidiyon, hukumar ta baza komarta inda ta bi sawun jarumar har ta kai ga kama ta domin fuskantar bincike.

Jarumar Kannywood, Samha Inuwa tana tsare a halin yanzu a ofishin hukumar dake Kano, inda jami'ai ke ci gaba da yi mata tambayoyi.

Dokar kare darajar kudin Najeriya

Hukumar ta nanata cewa cin zarafin Naira babban laifi ne a ƙarƙashin sashe na 21 na dokar babban bankin Najeriya (CBN).

Wannan doka ta haramta yaga kudi, takawa, lika kudi a taro, ko kuma kowane irin wulaƙanci ga takardun kuɗin ƙasa baki ɗaya.

EFCC ta ce:

Kara karanta wannan

Trump ya saki sunayen 'yan Najeriya 79 da za su fuskanci fushinsa

“Kowane ɗan ƙasa yana da nauyin kare darajar Nairar mu, kuma ba za mu lamunci duk wanda ya keta doka ba.”

Jarumar za ta ci gaba da zama a hannun hukumar har sai an kammala dukkan binciken da ake gudanarwa a kanta.

Samha M Inuwa tana fuskantar hukuncin daurin watanni 6 ko tara ko duka biyu kan wulakanta Naira.
Fitacciyar jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa da EFCC ta kama. Hoto: @samha_m_inuwa
Source: Instagram

Za a gurfanar da jaruma Samha a kotu

Hukumar ta sanar da cewa da zaran an kammala bincike, za a gurfanar da jarumar a gaban kotu domin yanke mata hukunci.

Idan aka same ta da laifi, ana iya yanke mata hukuncin zaman gidan yari na watanni shida ko tara mai tsoka, ko kuma haɗa su duka biyun, kamar yadda aka gani a hukunce hukuncen baya.

Wannan kamun ya biyo bayan jerin kama wasu fitattun mutane, ciki har da jarumai da mawakan Kannywood da aka yi a baya sakamakon watsa kuɗi ko wulaƙanta su.

A halin yanzu, Samha Inuwa ce jarumar fina finai a Najeriya ta baya-bayan nan da EFCC ta kama a cikin wannan shekarar ta 2026 bisa laifin wulakanta kuɗi.

Hukumar ta gargaɗi jama'a cewa tana sanya ido sosai kan duk wani bidiyo dake yawo wanda ke nuna raini ga takardar Nairar.

Kara karanta wannan

Malami ya dauki mataki na hana EFCC kwace kadarori 57 da ya mallaka a Abuja, Kano

Karanta sanarwar EFCC a nan kasa:

Wulakanta Naira: Kotu ta daure 'yan TikTok

A wani labarin, mun ruwaito cewa, an yanke wa wasu fitattun 'yan TikTok biyu, TobiNation da TDollar, hukuncin ɗaurin watanni shida saboda wulakanta Naira a Legas.

Hukuncin ya biyo bayan kama 'yan TikTok din tare da gurfanar da su da hukumar EFCC ta yi bisa zargin keta dokar Babban Bankin Najeriya (CBN).

Kotun ta amince da bidiyo da bayanan da EFCC ta gabatar da su a matsayin shaida, kuma ta yanke wadanda ake zargin hukuncin ɗauri, tare da zabin biyan tara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com