Bayan Shekaru 7, An Tuna Yadda Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Kusa Mutuwa a Jirgi

Bayan Shekaru 7, An Tuna Yadda Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Ya Kusa Mutuwa a Jirgi

  • A shekarar 2019, mataimakin shugaban kasa na wancan lokacin, Farfesa Yemi Osinbajo ya tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgin sama
  • Osinbajo ya gamu da hatsari ne a wani jirgi mai saukar angulu da ya dauko shi tare da hadimansa da nufin zuwa taron kamfe a jihar Kogi
  • A ranar, 2 ga watan Fabrairu, 2019 aka cika shekara bakwai da faruwar lamarin kuma tsohon hadimin Osinbajo ya tuna wasu abubuwa da suka faru

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Bayan shekaru bakwai, an tuna yadda mataimakin shugaban kasa na wancan lokacin, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi hatsari a jirgin sama a jihar Kogi.

A ranar 2 ga Fabrairu, 2019, jirgin sama mai saukar ungulu da ke ɗauke da Yemi Osinbajo ya yi saukar gaggawa bayan ya samu matsala a Kabba, jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Atiku ya yi ganawar sirri da babban Sanatan APC Abdulaziz Yari

Yemi Osinbajo.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo lokacin da zai shiga jirgin sama Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Source: Facebook

The Cable ta tattaro cewa Osinbajo na yawon kamfen ne a yankin Arewa ta Tsakiya domin neman goyon bayan jama’a ga tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, lokacin da lamarin ya a auku

A lokacin Buhari da Osinbajo na neman yan Najeriya su sake zabensu a karo na biyu domin ci gaba da ayyukan da suka fara.

Abin da ya faru da jirgin Osinbajo a 2019

A ranar da lamarin ya auku, Osinbajo ya hau jirgin helikwafta kirar AgustaWestland, mai lambar rajista 5N-CML, na kamfanin sufuri Caverton Helicopters Limited.

Jirgin ya tashi daga titi na 22 a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, da misalin ƙarfe 1:46 na rana cikin yanayi mai kyau.

Da misalin ƙarfe 2:20 na rana, wato kusan mintuna 30 bayan tashin jirgin, na’urorin jirgin suka faɗakar da matuƙan cewa na’urar sadarwa ta jirgi da sautin matuƙa ta lalace.

Da misalin ƙarfe 2:34 na rana, jirgin ya fado ƙasa da ƙarfi ta gefen ƙafarsa ta dama, sannan ya karkata gefe ɗaya. Duk da haka, Osinbajo da sauran fasinjoji 11 sun fito daga cikin jirgin lafiya ƙalau, babu wanda ya ji rauni.

Kara karanta wannan

Zargin lalata da matar aure: Magidanci ya sassara wani mutum da adda har lahira

Hadimin Osinbajo ya tuna abin da ya afku

Yayin tunawa da lamarin a wani sako da ya wallafa a shafin X (mai suna Twitter a baya) a ranar Litinin, tsohon mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, ya ce mataimakin shugaban kasar bai yarda an soke taron kamfen din ba.

Akande ya ce Osinbajo ne ma ya jagoranci tawagar zuwa filin kamfen cikin awa guda bayan faruwar lamarin.

“Cikin awa guda, Osinbajo ya jagorance mu muka koma filin kamfen. Bai yarda da shawarar a dakatar da taron, mu je mu huta ba. Wannan ya nuna jarumtaka da ƙudurinsa,” in ji Akande.
Jirgin Osinbajo.
Jirgin helikwafta lokacin da ya yi hatsari bayan dauko Farfesa Yemi Osinbajo Hoto: Professor Yemi Osinbajo
Source: Facebook

Wannan shi ne karo na biyu cikin watanni takwas da Osinbajo ya tsira daga hatsarin jirgin helikwafta.

A ranar 7 ga Yuni, 2018, wani jirgin helikwafta da ke ɗauke da shi daga Nigeria Customs Command and Staff College, Gwagwalada, Abuja, ya yi gaggawar sauka bayan mintuna kaɗan da tashinsa.

Osinbajo ya ba matasan Najeriya shawara

Kara karanta wannan

A karshe, an ji abin da ya taimaka aka gano shirin yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya buƙaci ƴan Najeriya, da su rika shiga harkokin siyasa domin amfani da ita a matsayin hanya ta samar da shugabanci nagari.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna cewa duk da mummunan suna da siyasa ke da ita a halin yanzu, ita ce kaɗai hanya halastacciya ta samun jagoranci.

Osinbajo ya bukaci matasa da su shirya kansu ta furkar ilimi da kyakkyawar dabi'a domin ta haka ne za su kawo gyara a harkar siyasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262