Jirgi dauke da Yemi Osinbajo ya yi hatsari - Ga bidiyon yadda jirgin ya fadi

Jirgi dauke da Yemi Osinbajo ya yi hatsari - Ga bidiyon yadda jirgin ya fadi

A jiya Asabar, 2 ga watan Fabreru, 2019, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa Jirgi mai saukar angulu wanda ya dau mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, sanata Ojudu, mataimakin shi na musamman da liktan matar shi ya rikito daga sama.

Hadarin ya faru ne a garin Kabba, jihar Kogi.

Kamar yadda labari daga babban mataimakin farfesa Osinbajo akan yada labarai, Laolu Akande, ya bayyana, hatsarin ya faru ne da tsakar ranar asabar. Osinbajo da sauran wadanda ke cikin jirgin na nan lafiya lau.

KARANTA WANNAN: Yan ta'adda sun tayar da tarzoma a yakin zaben APC, mutum 1 ya mutu, 2 sun jikkata

Kalli bidiyon yadda jirgin ya yi hatsari:

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel