Kotu: Yadda Tsohuwar Ministar Mai, Diezani Ta Samu Kuɗin Fantamawa a Birtaniya

Kotu: Yadda Tsohuwar Ministar Mai, Diezani Ta Samu Kuɗin Fantamawa a Birtaniya

  • Hukumomi a Birtaniya sun bayyana yadda tsohuwar Ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke ta samu kuɗin fantamawa
  • Sun yi zargin cewa arzikin ne suka tsaya mata, ana ɗaukar nauyin rayuwar Diezani a Birtaniya domin a ba su kwangiloli
  • Ana tuhumar ta da karɓar kayan alatu da kadarori a matsayin cin hanci yayin da take kan aiki a gwamnatin Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Great Britain – Sababbin bayanai sun fito a gaban Kotun 'Southwark Crown' da ke Landan, inda masu gabatar da ƙara na Birtaniya suka ƙaro hujjoji a kan tsohuwar Ministar mai, Diezani Alison-Madueke.

Sun bayyana yadda wasu manyan ’yan kasuwa a fannin makamashi, wadanda aka ba manyan kwangiloli daga Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), sun tila wa Diezani Alison-Madueke kudin rashawa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni, shugabannin jam'iyya sun zauna, an tsayar da lokacin babban taron APC

Diezani Alison Madueke na fuskantar tuhume-tuhume
Diezani Alison Madueke, tsohuwar Ministar mai ta Najeriya Hoto: Political Economist
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito masu gabatar da kara sun ce suna zargin ƴan kwangilar da ɗaukar nauyin rayuwar tsohuwar Ministar albarkatun man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, a Birtaniya.

Ana tuhumar Diezani Alison-Madueke da rashawa

Premium Times ta wallafa cewa masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotu cewa ’yan kasuwar sun rika biyan kuɗin kula da gidajen da Diezani ke amfani da su a Ƙasar Birtaniya.

A cewar ƙarar, Diezani tana fuskantar shari’a tare da wani jami’in mai, Olatimbo Ayinde, da kuma ɗan’uwanta, Doye Agama da ake zargi da hannu a rashawa.

Ana tuhumar su da laifuffuka guda biyar da suka shafi karɓar cin hanci ta hanyar kayan alatu da kuma amfani da kadarori masu tsada. Dukkansu ukun sun musanta zargin

Ana zargin Diezani Alison Madueke da karban cin hanci iri-iri
Tsohuwar Shugabar OPEC, Diezani Alison Madueke Hoto: Getty
Source: Getty Images

Mai gabatar da ƙara, Alexandra Healy, ta bayyana wa alƙalai cewa Diezani ta “rayu cikin alatu a Landan” ne bisa taimakon mutanen da ke neman samun ko ci gaba da rike kwangilolin mai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Hannatu Musawa ta yi gargadi kan ajiye Kashim Shettima a 2027

Ta ce an ba ta kadarori masu tsada da kayayyakin alfarma daga mutanen da suka yi imanin za ta yi amfani da tasirinta wajen fifita su a rabon kwangiloli.

Diezani: Abin da aka shaida wa kotu

Kotun ta kuma ji cewa Kolawole Aluko, wani hamshakin attajirin mai da jiragen sama, wanda aka ambace shi a wani ɓangare na tuhuma amma ba ya fuskantar shari’a a yanzu, ya kashe fiye da £2m a wajen sayen kayayyakin alatu ga Diezani a shagon Harrods.

An ce Diezani Alison Madueke tana da mai sayo mata kaya shagon, inda ta rika amfani da katunan biyan kuɗi na Aluko da kuma katin zare kuɗi na kamfaninsa, Tenka Limited.

Kotun ta ji cewa irin wannan matsayi a Harrods ana ba shi ne ga abokan ciniki da ke kashe sama da fam £10,000 a shekara.

An bayyana cewa Diezani da iyalanta sun rika zama a wani katafaren gida da ke wajen Landan, wanda Aluko ya saya ta hanyar wani kamfani kan fam £3.25m.

Ana zargin shi ne ya rika biyan kuɗin wutar lantarki, albashin ma’aikata da kuɗin gyare-gyaren gidan.

Kara karanta wannan

Tsofaffin 'yan majalisa sun yi watsi da mara wa Tinubu baya a zaben 2027

Healy ta jaddada cewa babu hujjar da ke nuna Diezani ta ba da kwangila ga kamfanonin da ba su cancanta ba.

Sai dai ta ce bai dace ba minista mai kan aiki ya karɓi wani tagomashi daga mutanen da ke kasuwanci da hukumomin gwamnati.

An kuma ambaci Aluko a takardun takardun Panama, tare da rahotannin bincike a kan zargin taimakawa wajen motsa kuɗin cin hanci da suka shafi Diezani.

Diezani Alison-Madueke ta rike muƙamin Ministar Albarkatun Man Fetur daga 2010 zuwa 2015 a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, sannan ta zama shugabar ƙungiyar OPEC a 2014.

Diezani Alison Madueke ta bayyana a kotu

A baya, mun wallafa cewa tsohuwar Ministar Albarkatun Mai ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, ta bayyana a gaban wata kotu da ke birnin Landan na Ƙasar Birtaniya.

Ta gurfanar a gaban Southwark Crown Court domin sauraron gabatarwar farko ta shari’ar da ake yi mata kan zargin cin hanci da ya kai £100,000.

Diezani ta gurfana a kotun ne a mataki na farko na shari’ar, inda ake tuhumarta da karɓar kuɗin cin hanci yayin da take rike da muƙamin ministar mai a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng