Jerin kayan ado kimanin 2000 na kudi $40m na Diezani Madueke da Gwamnati ta kwace

Jerin kayan ado kimanin 2000 na kudi $40m na Diezani Madueke da Gwamnati ta kwace

  • Gwamnatin tarayya ta samu nasara a kotun daukaka kara kan kayan adon tsohuwar ministar arzikin man fetur
  • Kayan adon da jami'an EFCC suka kwashe daga gidan Diezani Madueke sun kai $40 million a kasuwa
  • Jami'an EFCC sun bayyana cewa kudaden wadannan kayan ado sun fi karfin kudin albashin Diezani Madueke

Kotun daukaka kara ta amince da hukuncin sadaukar da kayan adon da darajarsu ta kai $40 million mallakin tsohuwar ministar mai, Diezani Allison-Madueke, ga gwamnatin tarayya.

Alkalin kotun dake zamanta a Legas, Festus Obande, a hukuncin da ya zartar yace babu gaskiya cikin kalaman Diezani kan yadda ta mallaki wadannan dukiyoyi, rahoton ChannelsTV.

A 2019, Alkalin babbar kotun tarayya/ Nicholas Oweibo, ya baiwa Hukumar EFCC damar mallakawa gwamnati dukiyoyin.

Kara karanta wannan

Masarautar Dansadau ta yi zaman sulhu da kasurgumin dan bindiga, Ali Kachalla

Diezani Madueke ta daukaka kara inda tace EFCC ba tada hurumin shiga mata gida tare kwashe mata dukiya ba tare da izini ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Diezani Madueke ga Gwamnati
Kotun daukaka kara ta tabbatar da sadaukar da kayan adon $40m na Diezani Madueke ga Gwamnati Hoto: F Carter Smith/Bloomberg
Asali: Getty Images

A cewar takardan kotu, wadannan kayan ado sun hada da:

"1. Warwaro masu tsada 419

2. Zobe masu tsada 315

3. Yan kunne masu tsada 304

4. Sarkar wuya masu tsada 267

5. Agogo masu tsada 189

6. Wasu yan kunne da sarka na daban guda 174

7. Sarkar hannu masu tsada guda 78

8. Brooches masu tsada 77

9. Dutsunan sarkar wuya masu tsada 78"

Lauyan EFCC ya bayyanawa Alkali cewa an yi zargin tsohuwar Ministar bata mallaki wadannan kayan ado da kudin halal ba.

Wani mai binicken EFCC, Rufai Zaki, ya bayyanawa kotu cewa kudaden wadannan kayan ado sun fi karfin kudin albashin Diezani Madueke.

Kara karanta wannan

EFCC: Ma’aikacin banki ya tona yadda tsohon gwamna da SGG suka 'ci' N1.5bn a 2015

Labarin rigar mama ta lu'u-lu'u a kayan Diezani: Shugaban EFCC ya yi karin haske

Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ya ce babu wasu rigunan mama da aka samo daga Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur.

Diezani, wacce ta hanzarta barin kasar nan bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mika mulki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015, an zarge ta da sace $2.5 biliyan daga gwamnatin tarayya yayin da ta ke minista, lamarin da ta musanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng