An Gano Jiha 1 da Tinubu Zai Iya Amincewa a Kirkira a Najeriya

An Gano Jiha 1 da Tinubu Zai Iya Amincewa a Kirkira a Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu na dab da amincewa da ƙirƙirar jiha guda ɗaya kacal daga cikin jihohin da 'yan majalisa ke fafutuka a kirkira
  • Anioma ce ke kan gaba a jerin jihohin da ake la’akari da su saboda wadansu dalilau da suka shafi zarginn wariya da kankantar jihohi a shiyya
  • Ana ganin matakin zai rage koken wariya da daidaita wakilci a Kudu maso Gabas da kabilar Ibo ke da shi a kan gwamnatocin Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na iya amincewa da ƙirƙirar jiha guda ɗaya kacal.

Zai tabbatar da natakin bayan an kammala dukkannin matakan doka a Majalisar Tarayya da majalisun jihohi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu 'ya amince' da kirkiro sabuwar jiha 1 a Najeriya, an bayyana sunanta

Ana sa ran Shugaban kasa zai aince da kirkirar jiha day
Shugaban Najeriya Bola Tinubu na sa hannu a kan wata takarda Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa majiyoyi daga Abuja sun bayyana cewa jihar Anioma ce ke samun karɓuwa sosai a matsayin jiha ta shida a yankin Kudu maso Gabas a wajen Tinubu.

Za a iya kara kirkira jiha a Najeriya?

Rahotanni sun nuna cewa tuntuba tsakanin manyan masu ruwa da tsaki ya kai wani mataki mai zurfi, musamman daga bangarorin da ke adawa da saka Anioma a cikin jerin jihohin Kudu maso Gabas.

Duk da haka, majiyoyi sun ce ra’ayin fadar shugaban ƙasa ya karkata ne ga Anioma, bisa la’akari da hujjojin adalci, daidaito da wakilci na siyasa

Ana sa ran kirkirar jihar daga Delta
Taswirar jihar Delta, inda ake sa ran fitar da jihar Anioma Hoto: Legit.ng
Source: Original

Anioma da ke yankin Delta ta Arewa, na samun goyon baya saboda ana kallonta a matsayin hanya mafi dacewa ta rage jin wariya da yankin Kudu maso Gabas ke ji ana yi masa.

A halin yanzu, yankin na da jihohi biyar kacal, mafi ƙanƙanta a Najeriya, lamarin da ya sa wakilan yankin ke fafutukar neman kari.

Kara karanta wannan

Kwanaki kadan da dawowa, Shugaba Tinubu ya sake barin Najeriya

Bola Tinubu ya karkata ga jihar Anioma

Wata majiya ta kusa da fadar shugaban ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu zai dauki matakin samar da Anioma don rage koke-koken Ibo.

Majiyar ta ce:

“Za a ƙirƙiri Anioma domin rufe gibin da ke akwai a Kudu maso Gabas da kuma rage koke-koken Ndigbo. Shugaban ƙasa ya fahimci muhawarar da ke tattare da batun, amma ya ga Anioma ce mafi yiwuwa a halin yanzu.”

Wasu kungiyoyi a Delta sun dage cewa ya kamata a ƙirƙiri Anioma a matsayin jiha a Kudu maso Kudu, lamarin da zai ƙara yawan jihohin yankin zuwa bakwai, amma ba su samu goyon baya ba.

Sanata Ned Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa, wanda ya dade yana jagorantar wannan fafutuka, ya bayyana kwarin gwiwa cewa an kusa cimma nasara.

A cewarsa:

“Wannan fafutuka ta tarihi ne da ba ta taba samun irin wannan kulawa da goyon bayan kasa baki ɗaya ba.”

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai gana da manyan masu ruwa da tsaki bayan tuntuba da shugabannin Majalisar Tarayya, wadanda ake cewa suna nuna goyon baya ga wannan tsari.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Sojoji sun mika rahoto kan jami'ai 16 da ake zargi ga shugaba Tinubu

Majalisa na duba yiwuwar kirkirar jihohi

A baya, mun wallafa cewa kwamitin majalisar dattawan Najeriya da ke kula da sauye-sauyen kundin tsarin mulkin ƙasa na shekarar 1999 yana aiki.

Ya bayyana cewa zai yi nazari kan ƙudurori 31 da ke neman a ƙirƙiri sabbin jihohi a faɗin ƙasar, bayan bukatun yan majalisu da dama na a waiwayi yankinsu wajen samar da karin jiha.

Sanata Barau I. Jibrin, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya ce za a tattauna waɗannan ƙudurori ne ta hanyar zaman jin ra’ayin jama’a da aka tsara gudanarwa na tsawon kwanaki biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng