Soja Ya Samu Rauni da Gobara Ta Kama Gidan Sojoji, Ta Kona Masallacinsu a Yobe
- Gobara ta tashi a wurin binciken sojoji da ke Potiskum a jihar Yobe, inda ta lalata dakuna da yawa da kuma wani masallaci
- Wani jami’in soja ya samu raunuka sakamakon gobarar, yayin da jami’an agaji suka yi gaggawar shawo kan lamarin cikin gaggawa
- Hukumar YSEMA ta ce ana zargin matsalar lantarki ce ta haddasa gobarar, kuma an fara bincike tare da tallafa wa wadanda abin ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Damaturu, Yobe - Wata gobara ta tashi a wurin binciken ababan hawa na sojoji a jihar Yobe lamarin ya jawo asarar dukiyoyi.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis 15 ga watan Janairun 2026 da rana wanda ta lalata dakunan kwana takwas da kuma masallaci da raunata wani daga cikin sojoji.

Source: Original
Yadda gobara ta kona masallacin sojoji
Rahoton Punch ya ce wutar ta kama ne a wata matattarar binciken sojoji da ke kan hanyar Gombe a karamar hukumar Potiskum ta jihar Yobe.
Majiyoyi sun nuna cewa wani jami’in soja ya samu raunuka sakamakon gobarar, inda aka garzaya da shi domin samun kulawar gaggawa ta lafiya.
Shaidun gani da ido sun ce an fara lura da gobarar ne da misalin karfe 1:30 na rana, lokacin da hayaki ya fara tashi daga yankin sansanin sojojin.
Nan take mazauna yankin da jami’an tsaro suka daga ja hankalin jama’a domin daukar matakin gaggawa.
“Mutane sun yi kokarin kashe wutar tun da farko, amma ta bazu cikin sauri. Hayakin ya yi yawa sosai, kuma gobarar ta shafi kusan dukkanin dakunan kwana.”
- In ji shaidun gani da ido

Source: Facebook
Gobara: Abin da hukumar YSEMA ta ce
Shugaban Kwamitin Gaggawa na Karamar Hukuma a karkashin Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (YSEMA), Ahmad Daya, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho.
Daya ya ce jami’an agaji sun dauki mataki cikin gaggawa, inda suka samu nasarar shawo kan gobarar.
Ya kara da cewa an dauki jami’in sojan da ya jikkata domin jinya, kuma ana shirye-shiryen tallafa wa wadanda gobarar ta shafa.
A cewar rahotannin farko, ba a tantance ainihin musabbabin gobarar ba, sai dai ana zargin wata matsala ta wutar lantarki ce ta haddasa ta.
Babu rahoton mutuwar kowa a lamarin, yayin da hukumomi suka ce bincike na ci gaba, haka kuma, Hukumar YSEMA na hada kai wajen samar da tallafi ga wadanda gobarar ta raba da matsugunansu, ciki har da wurin kwana da kayan bukata na yau da kullum.
Gobara ta kona masallaci mai tarihi a Lagos
An ji cewa shugabannin Musulmi a Lagos sun roki Gwamna Babajide Sanwo-Olu da ya jagoranci sake gina masallacin da gobara ta kone kurmus.
Masallacin da ake kira Shitta-Bey mai shekaru 134 ya gamu da iftila'in gobara wacce ta lalata a makon da ya gabata a jihar Lagos.
Sun bayyana lalacewar masallacin a matsayin babbar asara ga Musulmi, Jihar Lagos da kuma tarihi a Najeriya baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

