Kananan Yara 469 Sun Mutu a Jihar Kano, Bincike Ya Nuna abin da Ya Kashe Su

Kananan Yara 469 Sun Mutu a Jihar Kano, Bincike Ya Nuna abin da Ya Kashe Su

  • Aƙalla yara 469 ne suka mutu a Kano sakamakon rashin abinci mai gina jiki a farkon shekarar 2025, lamarin da ya gigita mutane
  • Bincike ya nuna cewa 51.9% na yaran jihar Kano suna fama da tsumburewar jiki saboda karancin sinadarai da abinci mai gina jiki
  • Gwamnatin Kano tare da hadin gwiwar UNICEF sun dauki wasu muhimman matakai domin sayen tunkarar wannan babbar barazana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Aƙalla yara 469 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon rashin abinci mai gina jiki a jihar Kano tsakanin watan Janairu da Yulin 2025.

Farfesa Ruqayya Aliyu Yusuf, daga sashen yaɗa labarai na jami'ar Bayero (BUK), ta bayyana hakan yayin wani taron bita ga manema labarai a birnin Kano.

An samu mutuwar daruruwan kananan yara a Kano a cikin watanni 6 kacal
Wata mahaifiya na dauke da yarinyarta mai fama da cutar cumburewar jiki a wata cibiyar kiwon lafiya da ke gundumar Dalam, jihar Borno. Hoto: STEFAN HEUNIS / Stringer
Source: Getty Images

Mace-macen yara a jihar Kano

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe wani uban daba a Kano da rikici ya barke tsakanin kungiyoyi 2

Bincike ya nuna kusan kashi 51.9 na yara a jihar suna fama da tsumburewar jiki, wanda hakan ke nuna cewa ɗaya daga cikin kowane yara biyu a jihar ba ya girma yadda ya kamata, in ji rahoton Daily Trust.

Farfesa Ruqayya ta bayyana cewa talauci, rashin wadatar abinci, da kuma rashin dabi'ar cin abinci mai inganci sune manyan dalilan da ke rura wutar mace-macen yara.

Ita ma Amina Ado Yahaya, ƙwararriya a fannin ilimin tsirrai, ta nuna cewa jihar Kano ce ke kan gaba wajen yawan yara masu ƙarancin nauyi da kashi 42.6.

Amina Ado Yahaya ta yi kira ga magidanta da su rungumi noman kayan lambu a gidajensu domin inganta abincin iyalansu.

Matakan da gwamnatin Kano ta dauka

Domin magance wannan annoba, gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta haɗa gwiwa da Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) domin samar da abinci na musamman mai gina jiki (RUTF).

Tun a watan Agustan 2025, gwamnatin ta ware naira biliyan ɗaya don sayen waɗannan kayan abinci, sannan ta ƙaddamar da shirin samar da maganin Azithromycin ga yara sama da miliyan uku.

Kara karanta wannan

Kano: Wasu yara sun fadi dalilin murna da rasuwar mahaifinsu bayan shekaru 20

Wannan magani na Azithromycin domin kare su daga cututtuka kamar nimoniya da zazzaɓin cizon sauro, kamar yadda kafar Voice of Nigeria ta rahoto.

Gwamna Abba Yusuf ya hada kai da UNICEF wajen ganin an kawo karshen mace-macen yara a Kano.
Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya na duba wani ajin makaranta da ya lalace. Hoto: @Kyusufabba
Source: Facebook

Gwamnatin Kano ta ba lafiya fifiko

Rahma Farah, shugaban ofishin UNICEF a Kano, ya jaddada mahimmancin kula da kwanaki 1,000 na farkon rayuwar yaro, domin sune ginshiƙin ci gabansa.

Gwamnatin jihar ta kuma ba da tabbacin cewa za ta ci gaba da ba da fifiko ga fannin lafiya a cikin kasafin kuɗin 2026 da aka sanya wa hannu kwanan nan.

A cewar gwamnatin Abba Yusuf, hakan ne zai tabbatar da cewa an rage mace-macen yara da kuma samar da ingantaccen ruwan sha da abinci ga dukkan al'umma.

Yara miliyan 17 ke fama da tamowa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai aƙalla kananan yara miliyan 17 da ba su samun abinci mai gina jiki a Najeriya.

Wani darakta a ma'aikatar lafiya, Dr Binyerem Ukaire, ya ce rashin samun abinci mai gina jiki ya zama gagarumar matsala duk kuwa da kuɗin da ake narkawa akan hakan.

Abubuwan da ke haifar da tamowa a Najeriya sun haɗa da rashin ciyar da yara abinci mai ɗauke da sinadaran gina jiki, rashin kiwon lafiya, ruwa da tsafta, da kuma talauci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com