Yadda wani likitan kasar Amurka ya warkar da masu cutar Coronavirus 500 da maganin zazzabin cizon sauro

Yadda wani likitan kasar Amurka ya warkar da masu cutar Coronavirus 500 da maganin zazzabin cizon sauro

- Vladimir Zelenko likita ne a kasar Amurka da ya hada maganin wanda yake ba mutane suna tashi daga muguwar cutar coronavirus

- Zalenko ya bayyana cewa, yana hadin maganin shi ne da wasu magunguna biyu na kasar Faransa da na Koriya ta Kudu

- A wannan maganin kuwa, a kalla mutane 450 zuwa 500 ne suka warke daga muguwar cutar duk da akwai yuwuwar maganin yana da illoli

Vladimir Zelenko, likita ne a kasar Amurka wanda ya bada labarin hanyoyin da ya bi wajen warkar da masu cutar coronavirus daruruwa da maganin zazzabin cizon sauro.

Zalenko ya yi ikirarin amfani da hydroxychloroquine wajen maganin cutar kuma majinyata 450 zuwa 500 ne suka warke.

A wata tattaunawa da ya yi da Rudy Guiliani, tsohon shugaban New York, likitan ya ce ya hada hydroxychloroquine da wasu magunguna biyu bayan ya gano cewa kasar Koriya ta Kudu da Faransa sun yi amfani dasu.

Ya ce kusan mako daya kenan da ya dauka yana taimakon masu cutar coronavirus a Kiryas Joel da ke New York kuma babu wanda ya rasa ranshi.

"Babu majinyacin da ya mutu sakamakon cutar a wurina. Na samu uku daga ciki suna dauke da ciwon lamoniya," yace.

KU KARANTA: Hotuna: Yadda aka binne wani mutumi da ya mutu a cikin motar da yafi kauna a duniya

"A kalla majinyata 450 zuwa 500 ne suka warke kuma kaso biyu cikin uku duk daga wani kauyen suke." Ya kara da cewa.

A kan yadda yake bada maganin, Zalenko ya ce: "Na hada maganin Faransa da na Koriya ne sannan na hada da hydroxychloroquine. Ina hadawa da Zinc da kuma Azithromycin."

Likitan ya kara da cewa baya ba masu cutar wadanda basu bayyana da manyan alamomin. Ya ce matasa ne suka fi tashi daga ciwon don garkuwar jikinsu na da matukar karfin bada kariya. A kan iya wahala a makonni biyu amma ana warkewa.

Amma kuma jaridar Washington Post ta bayyana cewa Zalenko ya ce akwai yuwuwar maganinshi ya kasance da wasu illoli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng